Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA ta hukunta Afirka ta Kudu saboda amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba a wasanta na neman cancantar buga gasar Kofin Duniya na 2026.
FIFA ta ce Afirka ta Kudu ta yi asarar wasan da ta buga da Lesotho na neman buga gasar Kofin Duniya na 2026.
Sanarwar ta FIFA ta ranar Litinin 29 ga Satumba ta ce, an yanke hukuncin ne saboda Afirka ta Kudu ta yi amfani da É—an wasan da bai cancanta ba.
Afirka ta Kudu ta ci wasan ne da ci 2-0 ranar 21 ga Maris a garin Polokwane, wanda a yanzu aka mayar da shi rashin nasara da ci 3-0.
Hakan na nufin ta koma mataki na biyu a rukunin C, ƙasa da Benin, saboda bambancin ƙwallaye.
A yanzu Lesotho za ta ci gaba da zama a mataki na biyar da maki tara a wasannin na ƙasashen Afrika masu neman cancantar buga kofin duniya mai zuwa.
FIFA ta ce Afirka ta Kudu ta saɓa dokar FIFA saɗara ta 19 ta Ɗa'a, sakamakon amfani da Teboho Mokoena, duk da cewa ɗan wasan ya samu yalon kati biyu a wasanninsu da Benin da kuma Zimbabwe.
0 Comments