Gwamnatin Nigeria ta ce daga ranar 6 ga Oktoba, babu É—alibin Nijeriya, daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in Æ™asashen waje, wanda za a amince ya yi NYSC ko hutar da shi ba tare da bin tsarin NERD ba.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da bin Æ™a’idojin Hukumar Tsare-Tsare ta Ilimi da Ajiyar Bayanai ta Nijeriya (NERD) a matsayin sharaÉ—i na tilas don samun damar shiga ko samun hutu daga aikin yi wa Æ™asa hidima (NYSC).

Ka’idojin sun tanadi cewa, daga ranar 6 ga Oktoba, babu É—alibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in Æ™asashen waje – wanda za a amince ya yi NYSC ko hutar da shi ba tare da bin tsarin NERD ba.

Sakataren Gwamnati Tarayya George Akume ne ya aika da wannan umarnin a cikin takarda ta musamman ga duka ma’aikatun gwamnatin Æ™asar a ranar Lahadi a Abuja.