‎KD PRESS ✍️
‎Hussaini Hussaini
‎Sheikh Zakzaky (H), dattijon malami ne da tun a matakin samartakarsa Allah Ta'ala ya yi masa baiwa ta musamman, ilimi, hikima, hankali da basira. Hatta a cikin sa’anninsa babu wanda ya kai shi.
‎Malamin da ya zarce dubban malamai ba kawai a Najeriya ba, har ma a faɗin Afrika. Maƙiyansa ma suna da tabbacin cewa shi mutum ne mai gaskiya da nagarta. Har ma Sheikh Bashir Alfurƙan ya shaida cewa, tun suna a jami’a Sheikh Zakzaky (H) ke koyar da su iziya (explanation) a cikin tsantsar ilimi.
‎Sheikh Zakzaky (H) ya bambanta da sauran malamai, ba wai kawai a Najeriya ba, har ma a duniya. Wannan ya nuna cewa Allah Ta'ala ya zaɓe shi a matsayin abin koyi ga al’umma.
‎Na koyi darussa da dama daga Sheikh Zakzaky (H). Abin da ya fi jan hankalina shi ne, yadda yake da courage wajen tsayawa a kan gaskiya duk da matsin lambar maƙiya. Haka kuma yana da unique style of leadership wanda yake ratsa zukatan mutane, musamman matasa. 
‎Duk wanda yake son fahimtar ma’anar gaskiya da jajircewa a rayuwa, to ya duba rayuwar Sheikh Zakzaky (H).
‎#ZakzakySymbolOfPeace