Yau Shekara 3 Da Kisan Ummita

A Rana Mai Kamar Ta Yau 17 Ga Watan Satumba 2022 Wani Dan kasar Sin (China) Mai Suna Mista Geng Quanrong aka zarge Shi Da Kisan Wata Budurwa Mai Suna Ummita A Birnin Kano Najeriya. 

Tuni Jami'an Tsaton Yansanda Sun kama mutumin da ake zargi Mista Geng Quanrong, bayan mutane sun damke shi a gidansu marigayiyar ranar Juma'a 17 Ga Watan Satumba 2022.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a da dare, inda Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.

Mahaifiyar Ummita, Hajiya Lami Sani Buhari ta ce mutumin da ake zargi da kashe 'yarta ya sha zuwa gidansu yana neman ganin Ummita, amma ba ta son fitowa.

Ta ce a ranar da lamarin ya faru, É—an Chinan da ake zargi ya sake zuwa gidan da daddare inda ya yi ta buga musu kofa, abin da ya tilasta wa mahaifiyar bude masa kofa, don jin abin da ke tafe da shi.

Uwar ta ce Mista Geng ya bangaje ta, ya kutsa kai cikin dakin Ummita, kuma da ganin ta sai ya zare wuka ya yi ta caka mata.
A Ranar 22 Ga Watan Satumba 2022 Ne Kotu ta aika da dan China da ake zargi da kisan Ummita kurkuku.

Ana zargin Mista Geng Quanrong da kisan matashiyar, lamarin da ya ci karo da sashe na 221 na kundin laifuka na jihar Kano, a cewar kotun.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano  ce  ta gurfanar da shi a gaban kotun.

Kungiyar Sinawa 'yan kasuwa a Najeriya ta yi alla-wadai da kisan da ake zargin Mr Quanrong ya yi wa Ummita.

KD PRESS TV ✍️