Dakarun rundunar bada agaji ta Red Cross, Reshen Zaria, sun gano gawar Marigayyiya Haneefa ‘yar shekara uku da ruwa ya yi awon gaba da ita da yayarta dake goye da ita bayan sun lume a iftila’in ambaliyar ruwa da ya rutsa da su a ranar talata 8 ga watan satumba, a garin Tudun Jukun, dake Tukur Tukur a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.
An tsinto gawar Haneefa ne a lahadin nan 14 ga watan Satumbar, shekarar 2025 da Karfe 11 da Yan mintoci bisa kokarin jami,an dakuma addu,ar Al,umma Allah ya jikanta yasa masu ceto ne.
©KD PRESS TV ✍️
0 Comments