A ci gaba da gudanar da gasar Maulidin Annabi Muhammad (S) na Halka_Halka, wanda Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) su ke gudanarwa a Da'irar Kaduna, yau ma Yan uwa na Halkar Imam Mahdi (Atjf) sun gudanar da nasu Maulidin.
Taron wanda ya gudana a layin bola Rigasa Kaduna, ya fara ne da bude taro da addu'ah, Bayan haka, masu tamsiliya sun yi tamsiliya, wanda wa'azi ce musamman ga Iyaye Maza akan sauke hakkin 'Yayansu Mata ta bangaren Hijabi. Daga bisani an gudanar da ziyarar Manzon Allah (S).
Bayan haka, an mika abin magana ga babban bako, Shaikh Rufa'i, wanda ya yi jawabi mai fadi dangane da Haihuwar Annabi Muhammad (S), sannan ya yi bayani sosai akan hada kan Musulmi da gujewa gaba da juna.Daga bisani, wakilin 'Yan uwa na Da'irar Kaduna, Malam Aliyu Umar Tirmizy ya gudanar da nashi jawabin akan Imam Ja'afar Assadik (As). Bayan kammalawarshi ne aka yanka Alkaki (Cake) guda uku, na Manzon Allah (S), Imam Sadik, da kuma na Masoya Annabi Muhammad (S).
Daga karshe An raba kayan masarufi ga marayu, Sannan aka raba walima, Daga karshe akayi addu'a Anyi lafiya antashi lafiya.
KD_PRESS
20/03/1447
14/10/2025
0 Comments