A safiyar Jiya Asabar 22/6/2024 ranekun tunawa da shahadar Dr. Ayatullah Bihishti da mataimakansa 72 da kuma ranar Shari'a, shugabanni da manyan jami'an shari'a suka gana da jagoran addinin Musulunci na juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
KD-PRESS tanyi duba ga wasu sassa masu muhimmanci daga jawabin da jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi, a lokacin ganawarsa da shugabanni da jami'an shari'a kamar haka:
1- Dole ne hukumar shari'a ta aiwatar da adalci cikin jajircewa ba tare da la'akari da wani abu ba.
2- Ya kamata a aiwatar da aiki ta yadda jama'a za su amince da bangaren shari'a a matsayin gidan adalci.
3- Kada alkalai su dogara ga tushen hakkin bil'adama na yammacin turai don yanke hukuncinsu.
4- Ziyarar gani da ido da shugaban ma'aikatan shari'a ke yi tana da fa'ida kuma wajibi ce, amma sai an bi diddigi don samun sakamako.
5- A wani bangare na jawabin Jagoran yayi magana ne da 'yan takara inda ya ce:
Shawarata ita ce tattaunawar da 'yan takara suke yi a gidan talabijin tare ko kuma maganganun da suke yi ko dai a kungiyance ko a daidaiku, kada wadannan kalamai da dan takara zai fada yazama abu da ne zai faranta wa makiya rai don samun nasara a kan abokin hamayya.
Kada ku faɗi kalmomi masu soyuwa ga maƙiya. Wannan batu ne mai mahimmanci. Wani lokaci ana iya fitar da wasu kalmomi ga wannan kasa ko al'umman ta, ko tsarin Jamhuriyar Musulunci ya zamo ya sanya makiya farinciki, wannan bai halatta ba. Kalaman da ake magana su zama kalaman da ba sa farantawa makiyan kasa, makiyan al'umma, makiya tsarin.
KD-PRESS 🌐
©23/06/2024
0 Comments