-Bin Muhammad
KD-PRESS 🌐
©24/6/2024
Wasu Kadan Daga Cikin Wasu Ayoyin Qur'ani Da Hadisai Wadanda Suke Nuna Hakan,
1, A cikin suratu Ma'ida aya ta 55 tana cewa majibincinku wanda biyayyarsa ta wajaba a kanku shine Allah, sannan kuma Annabinsa, sannan kuma wadanda suka yi Imani kuma suka bayar da zakka alhalin suna ruku'u, manyan malaman sunna duk sun kasance sun ce wannan ayar ta sauka ne akan Ali (a.s) shi ya bai wa mai tambaya (roko) zobensa yana sallah yayinda yake ruku'u, kuma ta sauka ne game wannan shugaban ne, kuma dangane da cewa idan wannan ayar mai daraja ta kasance game da Ali ce me ya sa akai amfani da kalmar jam'i aka ce wadanda ba a ce wanda ba, ta za mu ce akwai misalai da yawa a cikin Alkur'ani inda ake amfani da kalmar jam'i ga mutum daya, a cikin dukkan malaman Sunna babu ko mutum daya da ya ce ana nufin wanin Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne.
2, Wata ayar kuma ita ce aya ta 67 a cikin suratul Ma'idah, wadda take umurtar Annabi da ya isarwa da mutane abin da aka saukar zuwa gare shi daga Allah, kuma cewa in dai baka isar da abunda aka saukar gareka ba kamar baka isar da dukkan sakon da aiko ba ne kuma ka sani cewa Allah zai kare ka daga cutarwar da kuke jin tsoro daga jama'a. Itama wannan Ayar malaman Ahlus-Sunnah sun ce ta sauka ne a ranar Ghadir, daga nan ne Annabi (SAWA) ya gabatar da Ali (AS) a matsayin magajinsa. Taun daga nan zamu san cewa abun da aka umarce shi da ya isar abu ne da mutane zasu nuna martaninsu akai kuma hadari ne tun da Allah ya e zamu zan karrka daga Mutane yadda ba za su iya cutar da shi ba kuma wannan lamari ba zai zama wani abu ba face Imamanci da shugabancin al'umma.
3, Wata ayar kuma da tai magana akan Khalifancin Imam Ali As ita ce aya ta uku a cikin suratul Ma'ida, wadda ke cewa a yau kafirai sun yanke kauna daga iya ruguza addininku, don haka kada ku ji tsoronsu kuji tsorona, a yau na cika maku addininku kuma cika maku ni'imata kuma na yarde maku musulunci a matsayin addini sanannen abu kenan wani abu ya faru da har ya zamo cewa kafirai ba za su iya ruguza Musulunci ba kuma wannan abun ba zai zama wani abu ba face an gabatar da shugaban Musulunci bayan Manzo. Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama wanda shi ne Imam kuma zai kare Musulunci daga hannun kafirai kuma addinin Musulunci ya zama cikakke tare da Imamanci kuma mafi girman falalar Niima itace samuwar Imam kuma itace Ni'imar abin da Allah Ya ba wa mutane.
4, Wata aya ta 59 a cikin suratun Nisa'i da take cewa "Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Annabi da ma'abucin lamari daga cikinku, ko shakka babu ma'abucin umarni ba zai zama wani ba face Imami ma'asumi, saboda idan shugaba mai bada umarni ba ma'asumi ba ne, a wuraren da ya yi kuskure, dole ne a yi masa biyayya kenan, idan ya yi umurni da aikata zunubi, wato wajibi da umarnin Allah kar muyi zunubi kuma dole ne mu yi biyayya tun farko akan umarninsa kaga idan shugaba yayi umarni da yin sabo kuma muka aikata kaga amsamu cin karo kenan,
HADISAI KAN HAKAN
Hadisin Waki’ar Ghadir Khum hadisi ne da aka rubuta daruruwan littafai da suka kai sama da littafi 162 daga wanda suke kunshe da riwayoyin manyan sahabbai da tabia’ai wanda hadisin ya kai haddin matsayin tawaturi da ba za’a iya karyata shi ba. Wanda sahabbai kusan 120 ne suka ruwaici hadisin, wanda ba zaka samu yawan adadin masu ruwaioto hadisi kamar haka a wasu sauran hadisai da aka ruwaito ba. Kai koma rabin adadin masu wannan ruwayar a wani hadisin ba zak samu ba, domin maruwaita wannan hadisin suna da yawa matuka.
Idan muka dubi lamari ta wata fuskar zamu ga Annabin Rahama bai fadi wannan hadisin a tsakar gidansa ko a cikin masallacinsa ko a cikin wasu gungu kadan na sahabbansa ba, sai dai ya bayyana fadinsa yana mai shewa a cikin taron mutane da birnin madina bai ishe su, ya fadi hakan aciin taron mutane dasuke cikin falalin sahara mai fadi a mafi girman taro na musulunci da tarihi ya shaida a zamanin manzon Rahama (SAWA).
Ibn Sa’ad a cikin littafinsa Dabaqat juzu’i na biyu shafi na 171 ya ce: sai manzo Allah ya yayi niyyar fita zuwa aikin Hajji kuma ya shelantawa mutane da hakan, sai mutane masu yawa suka zo Madina domin suyi koyi da manzon Allah (SAWA) a hajjinsa.
Shima Ibn Hibban ya anbaci irin wannan maganar ta ibn Sa’ad a juzi’i na biyu na littafin Siqat shafi na 124.
Wanda wannan riwayar an curo ta daga hadisin Jabir wanda Imam Muslim ya kawo a cikin littafin Sahihinsa juzu’i na biyu shafi na 886 nambar hadisi ta 1218 babin hajjin Annabi (SAWA) in ya ce: Lalle manzon Allah (SAWA) ya zauna a Madina shekara tara sannan ya shelantawa mutane -yin hajji- a shekara ta goma da cewa: Lalle Manzon Allah (SAWA) yana da nufin fita hajji, sai mutane daywa suka shigo Madina dukkansu suna so ya zama sun koyi da Manzon Allah (SAWA) kuma sun yi aikata irin aikin daya aikata sai mutane suka fita tare da shi –Manzon Allah (SAWA)- har sai da suka zo Zul Hulaifa... sai Manzon Allah (SAWA) yayi sallah a masallaci Sannan ya hau tgauwarsa Quswa’u, har sai da taguwarsa ta daidaita da tafiya a akan sahara sai na duba iya ganina a gabansa da damarsa da hagunsa da bayansa ba wanda nake gani sai mahayi ko matafiya da kafa kawai.
Shi ma Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Almusannaf ya kawo cewa: sai jabir ya ce: sai mutane dayawa suka shigo Madina dukkansu suna son suyi koyi da manzon Allah (SAWA) kuma suyi aikata irin abunda ya ya aikata. A cikin littafin Musnadil Himyari 1288 daga jabir ya ce; An yi shelar hajji da cewa lalle manzon Allah (SAWA ya nason yin hajji sai Madina ta cika. -da mutane-.
A wani hadisin kuma na Jabir wanda Abu Ya’ala a Musnadinsa ya fitar da shi sau biyu a juzu’i na hudu shafi na 24 namba ta 2027 da kuma a juzu’i na sha biyu shafi na 106 namba ta 6739 Jabir ya ce: sai na duba gabana da bayana da damata da haguna iayakar ganina mutane ne kawai masu tafiya a kafa da masu tafe akan abun hawa.
Shima Ibn Shair ya fada a juzu’i na farko na littafin Uyunut Tarik shafi na 394 cewa: kuma Sahabbai dubu 100 ne dama sama da haka su kai Hajji tare da Manzon Allah (SWA) har sai da ya zamo wand bai taba ganin manzo ba kafinta ko bayanta sun yi hajji tare da shi kuma sun sabmu matsayin Sahabbanci da ita.
Sannan Sibd Ibnul Jauzi ya fada a cikin littfainsa Tazkiratu Khawasul Ummah acikin maganar dagane da hadisin Gadir Khum a shafi na 30:” ya kasance a tare da Manzon Allah (SAWA) akwai sahabbai da kuma larabawan kauye wadanda ssuke zaune a Makka da Madina da sukai kai mutum dubu 120 sune wadanda suka halarci hajji tare da shi kuma suka ji wanna zancen daga gares shi..
-Bin Muhammad
*KD-PRESS* 🌐
©24/6/2024
0 Comments