Mhd Ana Hizbullah✍🏼
KD-PRESS 🌐
©24/6/2024
In kuka lura sosai, zaku gane cewa duk sanda Manzon Allah (S) zai magana akan Imam Ali (As), yana danganta shi da kansa ne. Shi Imam Ali bashi da abokin gwaji sai Manzon Allah (S). Sakon kenan.
Kalli abunda Manzon Allah (S) ya fada na cewa Imam Ali (As) kamar Haroun ne a wajen Annabi Musa. Ba zaka gane sakon ba sai ka san mene matsayin Haroun a wajen Annabi Musa. In muka koma ayar da tayi magana akan dangantakar Annabi Musa da Haroun, Allah ya ce:
وَاجْعَل لِّي وَزِيرًا مِّنْ أَهْلِي
هارون أخي
اشدد به أزري
وأشركه في أمري
كي نسبحك كثيرا
ونذكرك كثيرا
Haka duk wata magana da Manzon Allah (S) ya fada akan Imam Ali zaka ga yana jingina shi ne gareshi. Yace babu mai son Ali sai wanda yake kaunarsa. Ya kara fito abun a fili, ya ce duk wanda ya zagi Imam Ali ko ya cutar dashi, ta kowane siga, shi ya cutar, shi ya zaga. Imam Ali ne kadai in aka zage shi Manzon Allah (S) aka zaga kai tsaye. Shi yasa masu kiyayya ga manzon Allah suke fakewa da zagin Imam Ali don sun san kamar Manzon Allah (S) suka zaga.
Mhd Ana Hizbullah✍🏼
*KD-PRESS* 🌐
©24/6/2024
0 Comments