Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©26/6/2024
19_Zhulhaj_1445

Zuwa ƙarfe 10:00am na safe duk sun gama shiryawa, sun yi tsaf abinsu gwanin ban sha'awa, babbar cikinsu, Aunty Fidda, ita  ce ta fara fitowa, cikin natsuwa da sanyin murya  ta ce "Me kuke yi ne har yanzu ba ku fito ba? kar fa lokaci ya ƙure ku hanzarta". Nan 'yan uwan su ka fito dukansu mazan su da matansu, kallon su ta  yi gaba daya, yayin da daddaɗan ƙamshin da su ke yi ya karaɗe gidan, kai da ka gansu kasan Nera ta yi kuka wurin shirya wannan lafiyayyen adon, Mazan sanye su ke da fari kuma lallausan yadi, kana ganinshi kasan babba ne, ga hula ƙube mai kyau sun ɗora saman kansu wanda ya sha gyara, sai agogo da su ka maƙala a tsintsiyar hannayensu, su kuwa matan ba wani ado su ka yi ba, amma saboda darajar da Allah ya yi wa Hijabi, sai su ka zama kamar taurari a sararin samaniya, tsayawa faɗin kyawun da wannan iyalan su ka yi ɓata lokaci ne.

Gaba ɗayansu su ka tafi ɗakin iyayensu, inda su ka shiga su ka gaishe da kowa, sannan ku ka fito su ka nufi gidan maƙofta, duk inda su ka nufa binsu ake da kallo, kamar waɗanda ba a taɓa gani ba.

Gidan Hajiya Maryamu su ka fara shiga, wadda ta kasance maƙwabciyarsu ta hannun dama,  Aunty Fidda ce ta umarci Sajida ta shiga  ta yi wa mazan iso zuwa gidan, bayan an ba su izinin shiga ne su ka shiga da Sallama ɗauke a bakinsu, cikin fara'a da farin ciki Hajiya ta tarbesu, ta na zolayarsu ta na faɗin" Aaah yau su Fidda ne a gidan namu? Wannan wanka haka kamar yau take sallah, ai ko ranar Sallar ba ku yi haɗuwa irin wannan ba". Su dai ba su ce mata komi ba, sai murmushi da ke ɗauke a fuskarsu mai bayyanar da farin cikin da ke zukatansu.

Bayan sun ajiye mata kulolin abincin da ke hannunsu, su ka sami wurin zama su ka zauna, sai babbar cikinsu, (Aunty Fidda) ta ce "Hajiya Mama ai wannan ranar ta fi  Salla babba da ƙarama daraja, ranar Edi ce amma ta fi sauran Edodi, itace ranar EDIL GHADEER  yau ne ranar da Allah (T) ya aiko Annabi Muhammad (S) da Nasabta Imamu Ali (As) a matsayin Khalifa bayan Annabi (S)".

Cikin Rashin ganewa Hajiya ta ce" Kai Fidda, ban gane me ki ke nufi ba, buɗe min bayani yadda zan fahimta".

Fidda ta gyara zama ta ce, ba ri na fara buɗe maki bayani dalla dalla yadda za ki gane, da jin wannan zance sai ga Yaya Mudassir ya fito(Ɗan autan Hajiya) domin shi ma ya ji sabon saƙon  da bai taɓa ji ba, Fidda ta ce" Ba ni da ilimin da zan faɗa maki ko rabi kan abin da ya shafi *EDIL* *GHADIR* ,amma dai zan faɗa maku abin da na sani, sai na haɗa ku da inda za ku ji komai yanda  za ku gane.

Kamar yadda ku ka sani, Annabi Muhammad (S) shi ne Annabin Ƙarshe cikin Annabawan Allah, to bayan Annabin, kun taɓa tunanin wa Annabi ya barwa mutane wanda zai rinka isar masu da saƙo bayanshi? Ko haka nan Annabi ya tafi bai bar kowa ba? haka nan za ayi ta tafiya ba wani wanda zai saita mutane a hanya madaidaiciya? Ba a zo karshen zamani ba kuma ace ba Annabi? Ba shugaban Al'umma?Idan haka ta kasance, Allah (T) ba  zai kama  mutane ba idan ba su yi addini ba, Hajiya ku yi tunani da kanku, Allah fa ba azzalumi ba ne, mai adalci ne.

Nan fa Hajiya ta yi shiru ta na tunani, da alama karatun ya na shigarta.

Aunty Fidda ta ci gaba da cewa, Saboda haka duk wani mai hankali kuma mai aikin hankali ba zai yadda cewa wannan ne Annabin Ƙarshe amma ba wani wanda zai isar da saƙonsa a bayansa ba. Wannan da nake faɗa maku shi ne Imamanci, Annabi ya bar 'ya'yansa su goma sha biyu a bayansa, wanda  Imam Ali shi ne farkon Imami bayan Annabi(S), kuma kowane Annabi ya na da wasiyyi, wanda kafin zuwan wani annabi zai rinka isar da sako, 

Cikin gamsuwa Hajiya ta daga kai, alamun ta fahimta, daga nan Fidda ta ci gaba da cewa" Menene Ghadeer Khum?

Ghadeer-Khum wani Muhalli ne wanda yake a mahadar dake tsakanin Makkah da Madina da wadanda suka taso taga Makkah zuwa garuruwansu, a kusa da wannan guri akwai wani kududdufi wanda ake kira da Ghadeer. Kusan zamu iya daukan filin Ghadeer a matsayin wani mahada (Junction) wanda daga wajen kowane mutum zai iya kama hanyar garinsu.

 Ghadeer shine muhallin da Manzon Allah (S) ya naɗa Imam Ali Bin Abu Ɗalib (As) a matsayin Khalifa a bayansa a ranar 18 ga watan Zulhijjah Shekaru goma bayan Hijirar Manzo (S). Ruwayoyi da dama sun tabbatar da cewa a wannan rana ne Manzo (S) yayi Hajjin sa na ƙarshe shi yasa ake kiran wannan Hajjin da 'Hajjin Bankwana' wato Hajjatul-wada.

 Kamar yanda Malaman Tafsiri na Mazhabar Ahlulbaiti sun kawo cewa Sahabban da suke halarci Hajji a wannan Shekarar sun kai kimanin 120,000. Malaman Tarihi sun yi bayanin cewa Manzon Allah sai da ya aika kowane garuruwa da saƙon Muslunci ya isa a wannan shekarar cewa kowa yazo aikin Hajji na wannan shekarar saboda ana son a isar da muhimmin saƙo kowa ya ji da kunnen sa kai tsaye.

 Bayan an kammala aikin Hajjin Shekarar ana hanyar dawowa Sai Manzo (S) yace kowa ya tsaya a dai-dai wannan muhalli na Ghadeer, bayan an tsaya yasa aka yi masa mumbari ya hau kai kowane Sahabi na ganin shi, sannan ya kira Ali Bin Abu Ɗalib (As) shima ya hau kan Mimbarin ya kaman hannun Imam Ali ya ɗaga sama, aka ce har ana ganin hammatotinsu, Manzo yake fadin "Mankuntu Maulahu Fa Haza Aliyu Maulahu" ma'ana wanda ya kasance ni Shugabansa ne to ga Aliy ya zama shugabansa .

 A wannan lokacin duk Sahabbai suka yiwa Imam Ali (As) bai'a suka miƙa wilayarsu gare shi duk da cewa a lokacin wasu Sahabban ransu ya ɓaci har wani yake cewa 'Ya Manzon Allah wannan saƙon daga gareka ne ko kuma daga Allah (S)?" Sai Manzo (S) yace daga Allah ne. A lokacin wannan Sahabin yace "Kazo kace mu bar bautan gumaka mun bari kace mu bar kaza mun bari, yanzu kuma kazo barin duniya kace kuma mu bi ɗan uwanka?" A nan take Allah (S) ya saukar da tsawa tayi ajalinsa.

 Bayan an kammala miƙa bai'a ga Imam Ali sai Allah (S) ya saukar da ayar suratul Ma'idah aya ta uku wanda sababul Nuzul dinta shine kan cikamakon saƙon Manzon Allah (S) ga al'umma. Kuma Manzon Allah ya bada sanarwar cewa duk wanda ya ji wannan saƙon ya sanar da wanda bai ji ba, uba ya sanar da ɗansa, ɗa ya sanar da jikansa har zuwa ƙarshen wannan duniyar. Har Manzo (S) ya tambaya Al'umma cewa "Na Isar muku da sakon" sai aka amsa da cewa "Eh" duk da akwai wasu Mutane da tun a lokacin suka murtuke fuska suka nuna baza su bi wannan wasiyyar ba wanda daga baya suka bijirewa hakan wanda shine ya jefa mu a halin da muke ciki yanzu.

Hajiya Mama, wannan saƙon ba saƙo ne na 'yan shi'ah zalla ba, sako ne na kowa da kowa, kuma wanda ya ji ya sanar wa wanda bai ji ba, Allah ya sani na sanar da ku abin da na sani a matsayinku na maƙwaftanmu, don  haka kuna da iliminku, yaya Mudassir kai ne ya hau kanka yanzu, ku ƙara bincikawa domin ku san asalin gaskiya, kar ku dogara da abin da na faɗa maku.

Murmushi dauke a fuskar Mama  da yaya Mudassir, Hajiya ta ce, Ni na taɓa jin wannan maganar a bakin mahaifina tun ban wuce shekara goma ba, amma da yake ya rasu kuma aka rarraba mu da 'yan uwanmu, inaga shiyasa ban sake ji ba, amma tun da yanzu kun tunatar da mu, za mu bincika mu gane gaskiya, Allah ya yi maku albarka Fidda ya baku mazaje na gari, ku kuma Hameed Allah ya baku mataye na gari masu ƙaunarku saboda Allah.

Tashi su ka yi don ci gaba da ziyarar Ghadeer, Hajiya ta ɗauki alheri mai yawa tai masu, ta na faman saka masu albarka, su ka yi sallama su ka tafi.

Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©26/6/2024
19_Zhulhaj_1445