Batula kmashi
KD-PRESS 🌐
©️26/6/2024
Imam Ali a cikin hadisai idan mutum ya bibiya ruwayoyi na hadisai zai ga cewa akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito da suke bayani dangane da falaloli da kuma darajoji na imam ali ga wasu daga ciki
An ruwaito daga Ummu salma ta ce naji Manzon Allah yana cewa, “Ali yana tare da Al-Qur’ani al-Qur’ani yana tare da Ali, ba zasu rabuba har sai sun sameni a tabki”
A wani hadisi kuma da aka ruwaito daga Abu zar ya ce: Manzon allah yace: “ya Ali duk wanda ya rabu dani ya rabu da Allah, duk wanda ya rabu kai hakika ya rabu da ni”
A wata ruwaya kuma Manzon Allah yace ma Ammar dan Yasir, ya Ammar biyayya ga Ali, biyayya ce gare ni, biyayya gareni, biyayya ne ga Allah ta’ala ya Ammar idan mutane baki daya suka bi wata hanya, Ali shi kuma yabi wata hanya to kabi hanyar da Ali ya bi kabar wan da mutanan su kabi.
Batula kmashi
KD-PRESS🌐
©️26/6/2024
0 Comments