Wasu Daga Cikin Kalubalan Da Na Fuskanta

Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©21/6/2024


Wata rana Yar Uwar Umma mai suna Yaya Yalwa, wadda take aure a Liman Katagum ta zo ganin gida, sai 'yan gulma suka tsegunta mata cewa Halima ta samo wata 'yar Inyamura. Ita kuwa daga jin haka sai ga ta a gidanmu ko hutawa ba ta yi ba. Lokacin ni kuma tafi makaranta. Umma ta tarbe ta da fara'arta irin ta dan uwan da suka dade ba su hadu ba. ta kawo mata ruwa da abinci ta ture su gefe daya ta ce, "ba ta su nake ba." Umma ta wara hannuwa, "lafiya dai. Yaya Yalwa na gan ki haka? Kowani abu ya faru ne?"
"Ina fa lafiya, na sami labarin kin rakito wata 'yar Inyamura, 'yar da babu wanda ya san asalinta?
Umma ta yi dariya. "Allah Sarki Fadima kike nufi?
Yarinyar kirki. ga ladabi." Yaya Yalwa ta ce "rufa min baki. kin san iyayenta?! Ko kin san garinsu? Wa ya sani ma ko'yar kungiyar asiri ce ta zo ta cutar da ku, ta gudu ta bar ku cikin damuwa?" Umma ta dakatar da ita. ta daga mata hannu, alamar surutun ya ishe ta haka.

"Haba Yaya Yalwa yaya za ki dinga aibata yarinya, alhali ba ki san ta ba, ba ki ma taba ganin ta ba? Yaya Yalwa ta mike tsaye ta nuna Umma da yatsa. "dole ne ki mayar da ita inda kika dauko ta!"
Umma ta yi ta mata bayani, amma a banza kamar ma tana zuba wa wuta kananzir. Ta ci gaba da cewa. "ai ga 'ya'yan Yaya Mato da ya rasu, me ya sa ba ki dauko daya daga cikinsu kin rike ba. idan ladan kike so da gaske? Umma ta mayar mata da cewa. "ai ya'yan Yaya Mato suna hannun Yaya Musa ,shi ya sa, kuma ma rikon irn wadannan ibada ne. Yaya Yalwa ta ci ga ba da cewa.
"wannan ma ai rashin kunya ne tunda kin fi karfin mijinki a kan wata 'yar arna. Umma ma sai ta mike tsaye tare da dafa kirjinta cikin damuwa da takaici. "Shi ya fada miki? Ba da izininsa na
dauko ta ba? Kumna wallahi daga yau kar ki kara ce mata'yar arna!" Yaya Yalwa ta ce ta fada din, duk abin da za a yi, a yi. Ana cikin haka sai ga ni na shigo. Tun daga zaure na fara jin maganganu sama-Sama. Na yi sallama na durkusa har kasa. na gaishe ta ba ta anmsa min ba. Sai cika take yi tana batsewa. Na gai da Ummana. Sai na ga duk hankalnta a tashe yake. Na karasa gaban Ummana, "Umma me yake faruwa?"

Sai kawai na ji ta ce:"rufe mana baki munafuka!" Umma ta ce. "don Allah duk abin da za ki yi min ki yi min, amma don girman Allah babu ruwanki da wannan baiwar Allah". Da yake Yaddikko ma ba ta nan ta kai Salma asibiti saboda zazzabin da ke damun ta.

```Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a```

Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba

Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©21/6/2024