Ga Wasu Hanyoyin Da Za A Iya Bi Domin Kiyaye Kamuwa Da Kwalara

Mabaruka Adullahi✍🏼
KD-PRESS 🌐
©22/6/2024


Ga Wasu Matakai biyar na kariya daga cutar kwalara

SHAN RUWA MAI TSAFTA

Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Amurka CDC ta bayyana cewa daga cikin hanyoyin da ake bi domin kiyaye kai daga kamuwa da kwalara akwai shan ruwan mai tsafta.

Hukumar ta buƙaci a rinƙa dafa ruwa da kuma ajiye shi a wuri mai tsafta kafin a sha. Haka kuma hukumar ta ce idan mutum zai sayi ruwan kwalba, ya tabbatar kwalbar a rufe take kuma mai inganci ce.

Yawan wanke hannu da sabulu da ruwa mai tsafta

Hukumar ta CDC ta bayar da shawara kan jama’a su rinƙa wanke hannunsu da sabulu da ruwa mai tsafta lokaci bayan lokaci.

Hukumar ta ce akwai buƙatar a rinƙa wanke hannu kafin da bayan dafa abinci.

Ta kuma ce wanke hannu bayan fitowa daga ban-ɗaki na da matuƙar muhimmanci da kuma bayan yi wa yara tsarki.

A GUJI YIN BAYA BA-HAYA A FILI

CDC ta yi gargaɗi ga masu ba-haya a fili kan cewa idan mutum ba shi da wurin da zai sauke larurarsa, ya tabbatar ya je wani wuri mai nisa daga ruwan da ake amfani da shi, sannan ya tabbatar ya binne ba-hayar da ya yi.

Hukumar ta ce ga masu gina masai na gargajiya a gidaje, su tabbatar sun gina shi aƙalla mita 30 daga matattarar ruwa.

         KULA DA ABINCI

Hukumar ta CDC ta yi gargaɗi kan cewa a rinƙa cin abinci da aka dafa shi da kyau ya dahu sosai.

Ta buƙaci a rinƙa wanke kayan lambu da na marmari sosai kuma da ruwa mai tsafta kafin a ci ko kuma a sha.

Haka kuma ta ce mutum ya guji shan kayan marmarin da ba shi ya ɓare su.

               TSAFTACE GIDA

Hukumar ta CDC ta buƙaci gida ya rinƙa kasancewa a cikin tsafta a kowane lokaci domin guje wa cutar kwalara.

Ta ce a rinƙa amfani da sabulu domin wanke wuraren dafa abinci da kuma barin su suna bushewa.

Haka kuma ta buƙaci a rinƙa wanke ban-ɗaki lokaci bayan lokaci musamman idan ba-haya ya ɓata shi.

Ta kuma buƙaci a rinƙa amfani da sinadaren kashe ƙwayoyin cuta domin wanke ban-ɗaki.

Ta kuma buƙaci tsumman da ake amfani da shi wurin goge-gogen gida a rinƙa wanke shi da kuma jiƙa shi a cikin ruwan zafi..

Mabaruka Adullahi✍🏼
KD-PRESS 🌐
©22/6/2024