Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©14/6/2024
Umma ta kasance mai yawan yin azumin Litinin da Alhamis. Na nuna mata kwadayina a kan ni ma zan kwatanta Ta ce, zan iya kuwa? Na ce mata zan iya. Litinin ta zagayo na dauki azumi. Ran nan kam na galabaita, na sha wahala sosai. sai da a ji kamar na fasa in ci abinci. Umma ta tausaya min. A ranar dai kaf ayyukana Umma ce ta aiwatar. Ranar ko makaranta ban shiga ba saboda tsabar na galabaita.
Da Alhamis ta zo, nan ma na ce zan yi. Ta ce in hakura in kara hutawa. Haka na yi da kadan-da kadan har na saba, bana jin komai. Har ba na kaunar a ce ina fashin sallah.
Wata rana ina dakin Umma ina mata shimfidar gado, sai muka ji sallama daga waje. Na mike, kaina babu ko dankwali a kan zan je in ga mai sallamar. Umma ta kira ni ta umurce ni da in dauki hijabi. Sai na ce mata, "ai iyaka ta bakin zaure." Ba ta ko sake kallo na ba balle ta ce nani kanzil. Ina ganin haka. na fahimci abin da take nufi, wato in dawo in dauki lullubina. na yi waje da sauri. Bayan na dawo ne nake gaya mata sakon mai sallamar cewa in Malam ya dawo a fada masa.
Ta zaunar da ni ta fara min nasiha tana cewa. "Musulunci ya yi wa mata gata. ya hana mu bayyanar da jikinmu. Ya umurce mu da mu dinga rufe jikinmu." Na tari numfashinta na ce, "jiki kuma Umma? Wannan kuma ai kowa yana rufewa." Ta gane me nake nufi. Sai ta yi dariya."rashin sani ya fi dare duhu." Ta ci gaba da yi min bayani. "ai mace dukkan jikinta abin suturcewa ne face fuskarta da tafukan hannayenta. Ta ci gaba da yi min bayani cewa, "kamar yadda Allah Ya yi umurni da yin sallah, haka ya yi umurni da suturce jikinmu. Na ce mata in Allah Ya yarda zan kiyaye.
Da ta lura da ni, ta ga ina kokari, sai ta saka ni a makarantar haddar AIkur'ani mai suna Tahfizul Kur'an.
```Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a
Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...
Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©14/6/2024
0 Comments