Wasu Daga Cikin Kalubalan Da Na Fuskanta
Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©13/6/2024
A gaskiya ina jin dadin zaman gidan saboda yadda da Malam suka mayar da ni tamkar'yarsu da suka haifa. Sai dai bangaren Yadikko ne take gwada min wasu halaye.
Duk ran girkinta ba na koshi saboda abinci kadan take zuba min. Ko magana za ta yi min, sai ta daka min tsawa. Umma ta lura da hakan, ta sanar da Malam abin da ake ciki. Da Malam ya ji, sai ya tara su a dakinsa. "don Allah na roke ku ku rike yarinyar nan amana. In kun san za ku wulakanta ta, gara a mayar da ita inda aka dauko ta." Ya yi masu fada cikin nasiha.
Umma ta mayar da hankalinta kacokaf wajen koya min mu'amalat da ibadat na addini. saboda kullum bayan mun yi sallar asuba. takan koya min karatun Alkur'ani da littafin Kawa'idi da Ahlari.
A bangarena ni ce mai yin wanke-wanke da share-share da wankan yara. Da zaran na kammala ayyukana zan ci gaba da bitar karatuna. Karfe biyu na yi zan shiga makarantar cikin gidanmu, wadda Umma take koyarwa. In mun taso kuma zan ci gaba da bitan abin da na koyo a makaranta. Duk inda na kasa, sai Umma ta tuna min. Ba a fi wata guda ba na gane baki sosai, har ina karatu da kaina. Saboda har da daddare nakan tashi in yi bita.
Akwai wata rana ina tankade duk da haka littafina yana gefe, ina dan leka shi a haka. Umma ta zo za ta debi ruwa, ta tsaya a kaina ta dinga rera mani kalmomin yabo da karfafa gwiwa irin yadda ta saba gaya min. Duk lokacin da na yi wata 'yar gwaninta takan ce. "Fadima 'yar kirki, ga karatu, ga tsafta, ga addini. ga ladabi da biyayya 'yar Umma." ldan tana fada min haka, sai in ji kunya ta kama ni kamar in nutse kasa. Kuma duk abin da Umma za ta yi tare muke yi ni da ita.
tana koya min a karance sannan ta zo ta nuna mina aikace. Kamar sallar dare idan mun yi yau, gobe ba za ta tashe ni ba sai jibi. Haka ta rika tarbiyyantar da ni har na saba yin (azkar) kamar salati da hailala da istigfari. har na riga na saba da yawaita karatun Alkur'ani. Takan yawaita min nasiha kamar haka: "Fadima ki dinga yawaita karatun Alkur'ani saboda zai buda miki kwakwalwarki ki rika fahimtar karatu sosai, kuma zai kara miki natsuwa
```Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a```
_Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba_ ...
Fatima Khamis (Journalist)
KD-PRESS 🌐
©13/6/2024
0 Comments