Batoul K/mashi

KD-PRESS 🌐
©3/5/2024

Lokacin da ake ture-turen shiga motar cikin gaggawa, sai da na zo kamar zan shiga sai na labe a gefe. na yi baya. na buya a cikin wata rumfar masu sai da dankali. Sai da na bari motar tayi
nisa sosai har ta bace na dai na ganin su, sai na fito na hau tafiya. Sai da na dan yi nisa na tari babur na ce da mai babur din ya kai ni inda zan samu motar komawa Bauchi. Ya tambaye ni tashar Bauchi? Na
amsa masa da eh.
Bayan ya sauke ni a tasha na tambayi kudin motar zuwa Bauchi aka ce min dari biyu da hamsin. Na duba 'yan kucdadena. na ga iyakacinsu ma kenan, na biya. Ina ta dar-dar, ina ganin kamar za su biyo su gan ni. Bayan mun shiga mota, tafiyar da ba ta wuce minti arba'in da biyar ba muka iso Bauchi.

Motar ta sauke mu a daidai gidan mai na Wunti. Na fito na rasa ina zan nufa. Na yi tunanin in koma Railway. amma na jl
Isoron kar iyayena su biyo sawuna su same ni. Ga shi da ma tun can
ni ba sanin unguwanni na yi ba saboda ba yawo nake yi sosai ba. Ga shi dare yana kara yi. Sai kawai na mike ban san ina zan nufa ba. Na yi ta tafiya har na iso wata unguwa. Sai na kara kutsawa. na ci gaba
da tafiya har na iso wani lungu. Na ga wadansu mutane a zaune a kan wani dakalin kofar gida, na karasa na gaishe su na tambaye su da cewa. "don Allalh ina ne gidan mai unguwa yake? Sai daya daga
cikin mutanen ya mike ya nuna min da yatsarnsa. "kin ga wancan gidan mai hade da masallaci?" Ina gyada kai, "na gan." "To. gidan kenan." Nayi godiya.
Na karasa gidan na yi sallama. Matar gidan ta amsa tana kallo na saboda irin shigar da na yi, dagani sai doguwar riga, sai hula a kaina ta sakakken bakin lilo, ga shi kafafina sun yi futu-futu da kura. ga yunwa ta galabaitar da ni. Na gaishe ta na tambaye ta "ko Mai unguwa yana nan"? Ta amsa mani da cewa. ki je ki ce yana
zuwa. A zaton ta ko aiko ni aka yi daga waje. Na ce mata wajen sa na zo. Fadin haka ya sa alamun mamaki ya bayyana a fuskarta. Ta taso da kanta ta wuce gaba ta kai ni, har kofar dakinsa. Ta yi sallama ya kai sau uku kafin ya amsa.

Da alamun barci yake yi. Ya ce: "lafiya?" Ta shiga ta bar ni a tsaye a waje, ina ji tana masa bayani, Ya fito dattijo da shi ya tambaye ni,"yarinya me ke tafe da ke cikin dare haka?

Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a

Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigab ...

Batoul K/mashi
KD-PRESS 🌐
©3/5/2024