Batoul K/mashi
*KD-PRESS* 🌐
©9/5/2024
Dattijon yafito ya tambayeni yarinya me ke tafe dake cikin dare haka?" Na durkuSa na gaishe shi. ya amsa min Na Sunkuyar da kaina kasa na ce da shi, "ina son zan musulunta ne" Ya sake tambaya ta. "daga ina kike?" Na ba shi labarin abin da ke tafe da ni.
A daren aka musuluntar da ni, aka ce in zabi sunan da nake so. Na ba shi zabin duk wanda ya dace. Ya ce, "ko kina so
Fadimatu?" Na ce, "na amince.
A ranar na yi barcin farin ciki. Na yi godiya ga Allah da ya cika min burina.
Zuwa can kuma tuanin iyayena ya fado min. Na ce ko yaya za su yi lokacin da za su farga ba na cikin notar? Olho.
Washe gari da hantsi, Ayya (kamar yadda na ji ana kiran ta) ta umurce ni da in tscfe kaina. in wanke shi domin ta yiminkitso.
Tana cikin yi min kitson ne sai muka ji sallama. Na daga kaina, sai muka yi ido biyu da wata doguwar mace fara tana sanye da doguwar riga mai alar ruwan kasa. ta dora hijabinta a kai iya gwiwa, shi ma kalar doguwar rigar. Bayan sun gaisa da Ayya, ni ma na gaishc ta. Aka ba ta tabarma ta zauna. Sai ta tambayi Ayya,"ko
yaron da na turo ya tambaya min kitso ya zo?" Ayya ta cc mata, "Eh ya zo shi: bari na karasa mata sai in yi miki"
Tana gama min sat na mike na debo ruwan sha na zo na durkusa har kasa na mika mata ruwan na wuce cikin dakin na
dauki shinkafa na fara regewa. Na ji bakuwar tana tambayar Ayya.
"ina kika samu 'yar Inyamura?" Ayya ta yi mata bayanin yadda aka yi na zo hannunsu. Bakuvwar ta ce, "na yaba hankalinta, idan na koma gida zan gaya wa Malam. Idan ya amince zai zo ya tanbayi
Mai unguwa, in ya yarda ina son ta zaunaa wajena."
Hakan kuwa aka yi. Ya zo ya tambaya aka ce, sai an yi shawara. Bayan kwana uku Ayya ta sanar da ni. Na shirya ta raka ni
gidan matar da ta zo kitso. Har na nuna damuwa a fuska saboda shakuwar da muka yi ta kwana biyu. Tace; kar na damu, wai ta ga alamar ni mai son karatun addini ne. Ta ci gaba da cewa,"za ki fi jin dadi a wajenta domin ita Malama ce har tana da makarantar Islamiyya a gidanta na matan aure da 'yan mata."
Bayan mun fito ne take ce min sunan unguwar da za mu unguwar Yakubo Wanka. Na tambaye ta sunan unguwar da muke yanzu fa? Ta ce, unguwar Makali. Bayan mun dan kukkutsa 'yan
Batoul K/mashi
KD-PRESS 🌐
©9/5/2024
Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a
Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...
Batoul K/mashi
KD-PRES 🌐
©9/5/2024
0 Comments