Batoul K/mashi

KD-PRESS 🌐
©2/5/2024

Wata rana ina kasuwa na baro Mamana a gida, ina bude shago, sai na ji makwabcinmu wanda ke daura da shagonmu, ya sa kasect mai dauke da tarihin Annabi Muhammad (S.A.W). yadda ya sha wuya matuka gaya, shi da sahabbansa a hannun makiya a farkon fara kiransa zuwa ga Musulunci har zuwa karshen rayuwarsa'. Sai na ji tausayinsa ya kama ni. Na ji hawaye na gudana a kumatuna. Wannan shi ya kara mini kwarin gwiwa a raina, "na ce koya za a yi. babu gudu babu ja da baya. Bayan na koma gida, sai na fara tunanin shin in gudu ne ko in tsaya a yi wadda za a yi? 

Tunanin Haulatu ya fado min. Na yi da na sanin rashin bin ta Abuja da ban yi ba.

A gida da daren wannan rana ina kwance a dakına sai naji mahaifiyata ta nufo dakin, Na rufe ido, kamar ina barci. ta kira ni taji shiru, sai ta koma baya, ba ta shigo inda nake ba. Ta koma dakin shakatawa ta iske Mahaifina, ina ji sun fara shawara a tsakaninsu cewa gara su nemi sauyin wajen aiki kar in zo n fi karfinsu. Har suka garma shawararsu ina sauraron su daga inda nake kwance. Da gari ya waye. sai na nuna kamar ban ji tattaunawarsu ba.

Ranar Lahadi da ni aka je coci. amm na ware gefe daya ban yi abubuwan cocin ba, har aka tashi muka taho gida tare.
Sun yi ta shirye-shiryen tashi na komawa garinmu ba tare da sun shaida mani ba: har ana gobe za a koma sannan suka ce da ni, "zamu koma garinmu." Da jin haka sai na hau murna. har ina cewa, "daman rabona da garin tun wani zuwan da nuka yi bikin kirsimeti, ban sake zuwa ba." Nanuna musu kamar ni ma ina son komawa. Washe gari da yamma muka je unguwar lgbo (quaters) inda ake shiga motar zuwa kudu. Bayan an gama komai mota ta tashi. mahaifina yana daga gaba. yayin da ni da mahaifiyata muke daga can baya, ina manne da ita kamar da gaske Nikadai na san irin abin da nake sakawa a cikin
zuciyata. Mukaci gaba da tafiya har muka iso Jos. ga shi lokacin magari ya yi, wurin ya fara duhu. Sai aka tsaya domin a ci abinci.

Bayan munkammala, sai na ga mahaifina ya matsa can gefe kadan yana sayen jaridar THE GAME. da yake shi ma'abocin kwallo ne. Da na ga hankalinsa ya karkata ga mai jarida na ce wa mahaifiyata.
Mama idan an koma cikin motar nan zan zauna kusa da Babana. Ta daga min kai, alamar amincewarta. 

Na fakaice ta na taba aljihuna naji had yanzu kudin da makwabtanmu gida da na kasuwa suka bani suna nan, sai nayi murmushin farin ciki. Kowa ya gama abin da yake yi. yayin da direban motar ya danna abin da ke alamta kowa ya shigo da gaggawa domin aci gaba da tafiya.

Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a

Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...

Batoul K/mashi
KD-PRESS 🌐
©2/5/2024