Batoul K/Mashi
Kaduna Press
©25/4/2024

cikin annashuwa sai nake tambayar Mahaifina, mencne ya sa mu ba ma yin tsarki irin na musulmai? Kwatsam, sai na ga ya hada fuska ya murtuke kamar ba shi bane muke wasa da dariya yanzu.
Mahaifiyata kuwa daman mun fi kusa da ita tana mikewa sai na ji saukan mari a fuskata tas! Sai da na ga wasu taurari sun gilma ta cikin duhu. Bakina ya fashe ya rika zubar da jini. Ta ci gaba da zagi na tana cewa, "Shi ya sa duk Lahadi sai ki kama ciwon karya?" Na yi ta ba su hakuri, musamman ma Mahaifina wanda yake ta faman fada. Na ce musu, "ni tambaya nake yi, ya kanmata ku ba ni amsar tambayata." Ta amsa mani a fusace, "idan amsar tambaya nake nema, to in bari sai ranar Lahadi in je in yi tambayar a inda za a bani amsa. Da ranar Lahadi ta zo na shirya na dauki Bible dina. Muka fito da iyayena, har muka isa babu wanda ya ce da wani kanzil. Mun isa daidai lokacin an yi addu'a har an fara jawabi. Gama jawabin ke da wuya, sai kida ya fara tashi, kowa ya mike sai rawa yake. Tuni ni kuwa dama na kosa. Kwatsam sai na fice kanmar zan zaga bandaki, sai na zarce gida. Na yi kwanciyata a gida. Can wani lokaci sai ga mahaifana sun dawo. Mahaifiyata tana karasowa ta daga labulen kofar ta gan ni kwance a doguwar kujera. Ta kama baki cikin mamaki, "dama gida kika gudo?" Na amsa mata da ban jin dadi shi ya sa. Ko saurarona ba ta yi ba ta dauko wayar wuta ta fara duka na kamar ba za ta bar ni ba. Na yi kuka kamar raina zai fita, har na yi tunanin ko tana kokarin raba ni da rayuwata ne. Da Mahaifina ya ga dukan ya yi yawa, sai ya zo ya karbe ni, yana mai tunatar mata da cewa ba ni da lafiya. A haka ta ci gaba da zagi na, ni kuma na lafe a jikin Mahaifina, jikina ya yi rudu-rudu. Daga ran nan na fara ganin sauyi. Ta daina kula ni. Hirar da muka saba yi da ita, yanzu sai dai mu yi da Mahaifina. Da yake shi mutum ne mai saukin kai. Wata rana ina kasuwa na baro Mamana a gida, ina bude shago, sai na ji makwabcinmu wanda ke daura da shagonmu, ya sa kasect mai dauke da tarihin Annabi (S.A.W). yadda ya sha wuya matuka gaya, shi da sahabbansa a hannun makiya a farkon fara Kiran Sa.
kiransa zuwa ga Musulunci har zuwa karshen rayuwarsa'. Sai na ji

Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a

Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...

Batoul K/Mashi
Kaduna Press
©25/4/2024