Ƙungiyar Hamas ta ce "haukan da masu ra'ayin Yahudanci" suke yi na kai hari a kan Falasɗinawa fararen-hula a Gaza na nuna gazawar rundunar sojin Isra'ila a yayin da ake yi mata turjiya.
"Haukan da masu ra'ayin Yahudanci suke yi a kan fararen-hula alamomi ne na gazawar sojojin mamaya kwata-kwata a yayin da suke fuskantar turjiya,'' in ji shugaban Hamas Izzat al Rishq a sanarwar da ya watsa a shafin Telegram.
Ya ƙara da cewa "Hotunan da aka ɗauka a Asibitin Shifa da ke Birnin Gaza sun nuna sojojin mamaya na ƴan Nazi suna yin kisan ƙare-dangi mafi muni a duniya a ɓangaren kiwon lafiya.''
Ya Æ™ara da cewa, “Goyon bayan da Amurka da Æ™asashen Yamma suke bai wa haukan da masu ra'ayin Yahudanci suke yi bai sauya ba wajen faÉ—aÉ—a rikici a wannan yankin."
0 Comments