Haulatu Ta rako ni har bakin hanya na hau kabu-kabu, ina hango Haulatu tana share kwalla. Ni ma sai na ji hawaye suna zubo min, muka rabu muna daga wa juna hannu. Da yake yanzu mun gama makaranta, sai na ci gaba da kula da shagon mahaifiyata. Amma yanzu abin da ya fi damu na shi ne
yaya zan yi na shiga Musulunci? Har mahaifiyata ta lura da akwai abin da ke damu na. Ta tambaye ni menene yake damu na? Ashe Mahaifina shi ma yana nan. Da ya ji tattaunawar da muke yi sai ya
fito, ya tambaye ni kamar yadda ita ma ta tambaye ni. Gaba daya sun zuba mani ido suna jiran in ba su amsa, "Ina tunanin sakamakon fitowar jarabawata na.
Tunanin ya ci gaba har ya fara sa ni ramewa. Sai mahaifina ya ce da mahaifiyata ta kai ni asibiti a duba ni, atabbatar da abin da ke damu na.
Mamana ta kai ni asibitin Railway, Likita ya yi mani tambayoyi, na amsa masa da cewa babu inda yake min ciwo. Likita ya sanya mana abin gwaji a kirjina da cikina da bayana. Ya gama yan gwaje-gwajcnsa ya juyo ga Mahaifiyata wadda take tsaye a
gefe. Ya ce babu wani ciwo da yake tattare da ni. Sai dai rashin cin abinci da yawan tunani. Bayan mun dawo gida take shaida wa Mahaifina yadda aka yi. Wannan ya sa ya kira ni ya kama hannuna, ya zaunar da ni a kujerar da ke fuskantar sa, ya ce in fada masa me nake tunani? Na amsa da cewa in dai ban ga sakamakon jarrabawata ya fito ba hankalina ba zai kwanta ba. Ya karbi takardar ya je ya
sayo mini magungunan ya hado mini da lemon kwali wajen kala hudu da 'crate' din kwai da kayan marmari ya ce da mahaifiyata cikin wasa, "Saura ki sha mata, sai na miki bulala", yana fada yana dariya. Ya ce kada na damu ya san takardata za ta yi kyau. Wadanda ba su da kokari ne suke fargabar jarrabawa. Mahaifina haka ya ci gaba da dawainiya da ni, duk ran da yake da kudi yakan sayo mani nama ko kifi. amma duk ran da ya sayo mani naman kare ko na alade ba na ci, sai in ji kamar zan yi amai. Tun lokacin da Haulatu ta sanar da ni cewa musulmai ba sa ci na ji na kyamace su. Duk ran Lahadi ba na zuwa coci sai dai na yi
karyar bani da lafiya. Ni dai kullum ina cikin tunanin yaya zan yi na yi sallah?
Wata rana bayan mun yi kalaci, muna hira, da na ga suna
Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a
Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...
Batoul K/mashi
Kaduna Press
©19/4/2024
0 Comments