Yarima Farhan ya gaya wa Antony Blinken cewa Saudiyya tana yin abin da ta ga ya dace ne ba domin an tursasa mata ba. 

Saudiyya ta ce yana da muhimmanci ta kyautata dangantaka da Isra'ila mai makwabtaka "saboda ci-gaban yankin" amma hakan ba zai yiwu ba sai an tabbatar da "martaba da adalci" ga Falasdinawa.

Ministan Harkoki Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken wanda ke ziyara a kasar.

"Idan ba a sama wa Falasdinawa zaman lafiya ba, idan ba a magance matsalolin da suke fama da su ba, duk wata kyautata alaka tana da iyaka," in ji shi.

Yarima Farhan ya bai wa Amurka shawarar mayar da hankali wajen ganin an samu kasashe biyu - Isra'ila da Falasdinu - domin kuwa hakan ne zai zama adalci ga Falasdinawa.