A safiyar yau Juma'ah 5/4/2024 dai-dai da 26/Ramadan/1445H Da misalin karfe goma na safe (10:00am) Almajiran Sayyed Zakzaky na Kaduna da sauran al'uma masu kishin Dan adamtaka suka fito kan titin Ahmadu bello way domin gudanar da muzaharan nuna alhinin da kin amincewa da zalunci Israel ga jama'ar Palestine ba dare ba rana. Muzahara dai ya tafi cikin tsari in da a ka daga daga katsina round about na katsina road a kafi lebentis zuwa bakin dogo,

zuwan jami'an 'yan sanda ke da wuya dai dai kano Road suka fara harba Harsha shi masu Rai kan Al'umma ba ji bagani, 
sun harbi mutane da daman gaske 

 zuwa hada wannan rahoton ana da tabbacin  mutum hudu Shahidai, masu rauni kuma mutum ishirin (20).

Ku kasance da Shafin KD PRESS Domin samun cikaken Rahoton yanda waki'ar ta kasance.


KD PRESS
©5/4/2024