A yau Asabar 6/4/2024 da misalin karfe 12:30pm, a ka gudanar da Jana'iza Shaheed Ibrahim Rabi'u, Mahmud Umar, Mustafa Aliyu, Haidar Ishaq, Hudu (4) cikin biyar wadan da jami'an 'yan sanda Nigeria suka kashe a jiya juma'a 5/4/2024 a yayin gudanar da muzahar nuna alhini ga Raunanan al'ummar Palestine a garin Kaduna.
Wakilin Yan uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky na da'irar Kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizy) ne ya jagoraci Sallar a Fudiyya Rimi da ke Rigasa Kaduna. Kammala Sallar ke da wuya a ka garzaya da su makwancin su da ke Darur rahama da ke danbo Zaria city, inda Malam Abdulhamid Bello ya tarbe su. An bizne su aka gudanar da addu'o'i.
Muna rokon Allah a amshi shahadar su ya baiwar iyalansu hakurin wannan rashi.
KD-PRESS
©6/4/2024
0 Comments