Rundunar ƴan sandan jihar Oyo da ke kudancin Nijeriya ta ce nan gaba kaɗan za ta gurfanar da mutanen da ta kama bisa zargin fafutukar kafa ƙasar Yarbawa a gaban kotu.
A ranar Asabar da ta wuce ne, ƴan sanda suka kama ƴan kungiyar bayan mamayar da suka yi wa Ofishin gwamnar jihar Oyo da kuma majalisar dokokin jihar suna sanye da kakin soji kuma riƙe makamai daban-daban da kuma tutar ƙasar da suke son kafawa.
Kazalika rahotanni sun ce mutanen sun yi yunƙurin kutsa kai cikin ofishin gwamnan jihar, amma jami’an tsaro su fatattake su tare da kama da dama daga cikinsu.
Ana zargin matar hamshakin ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan siyasa, marigayi Cif Moshood Abiola, mai suna Dupe Onitiri- Abiola da ɗaukar nauyin masu fafutukar bayan wani bidiyo da ta wallafa wanda ya karaɗe shafukan intanet, tana mai iƙirarin ɓallewa daga Nijeriya da kuma kafa shugabancin ƙasa ga al'ummar Yarbawa.
Ta'addanci
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo, Hamzat Adebola, ya bayyana lamarin a matsayin laifi da rashin kishi da cin amanar ƙasa da kuma ayyukan ta’addanci a yayin da yake gabatar da mutanen da ake zargi a gaban 'yan jarida, yana mai cewa ''za a hukunta su bisa tanadin doka.''
“Da farko ƴan sanda sun gargaɗi masu fafutukar da su watse amma sai suka yi kunnen-ƙashi daga nan gangaminsu ya juya zuwa rikici sai suka buɗe wuta kan ‘yan sanda da kuma tawagar jami'an sa-kai na Amotekun da ke wurin,” a cewar kwamishinan.
''An ƙwato bindigogi masu sarrafa kansu guda biyar da wasu tarin makamai da kayan sojoji guda 72 da harsashai 405 da dai sauransu," in ji Kwamishinan ƴan sandan.
0 Comments