Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bai wa kowane maniyyaci daga Jihar Kano tallafin naira dubu É—ari biyar domin cika kuÉ—in Aikin Hajji.
Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON ta buƙaci kowane maniyyaci wanda ya biya kafin alƙalami a baya ya cika aƙalla naira miliyan 1.9.
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, gwamnan na Kano ya ce a yanzu kowane maniyyaci daga Kano naira miliyan 1.4 zai bayar ga hukumar alhazan maimakon miliyan 1.9.
“Bayan Æ™arin miliyan 1.9 na kuÉ—in Aikin Hajji da Hukumar Alhazan Nijeriya ta yi, na amince a bai wa kowane maniyyaci daga Kano N500,000 domin tafiya Saudiyya.
“Dangane da haka, maniyyatan da suka biya kafin alÆ™alami a baya na miliyan N4.7 da miliyan N4.5 ga hukumar alhazan jihar a halin yanzu za su cika miliyan N1.4 maimakon miliyan N1.9,” in ji gwamnan.
Tun da farko dai Hukumar Alhazan Nijeriyar NAHCON ta Æ™ara farashin kujerar Aikin Hajjin bana da miliyan N1,918,032.91, inda ta bai wa maniyyata wa’adin zuwa 28 ga watan Maris É—in 2024 su biya cikon kuÉ—in.
Hukumar ta NAHCON ta ce an samu wannan ƙarin ne sakamakon ƙaruwar farashin dala a Nijeriya.
Sai dai hakan ya jawo martani da dama daga faɗin ƙasar inda aka yi ta kira ga gwamnatin ƙasar ta sassauta.
0 Comments