Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wa Majalisar Dokokin Kano sunan ɗan tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso domin tantancewa a matsayin kwamishina.

Mustapha Rabiu Musa na daga cikin sunayen mutum huɗu da gwamnan ya miƙa wa majalisar domin tantance naɗin muƙaminsu a matsayin kwamishinoni.

Sauran sunayen waɗanda aka miƙa wa majalisar sun haɗa da tsohon Kwamishinan Filaye da Saliyo da aka kora, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, Alhaji Abdul-Jabbar Umar Garko da Shehu Usman Aliyu Karaye.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Majalisar Dokokin Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar a wannan Talatar.