Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar  Abdourahamane Tiani ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin na Rasha inda suka yi magana kan hadin gwiwar tsaro.

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya tattauna ta wayar tarho a ranar Talata da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin game da "ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro", a cewar sanarwar da aka fitar a hukumance.

Tuni dai ƙasashen biyu suka amince a watan Janairu domin ƙarfafa alaƙar soji a lokacin da Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine ya jagoranci wata tawaga zuwa birnin Moscow.

Nijar ta kasance kan gaba a haɗin gwiwa da Ƙasashen Yammacin Duniya wajen yaƙar masu tayar da ƙayar-baya a yankin Sahel, amma ta rungumi Rasha a matsayin sabuwar abokiyar tsaro tun bayan hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a bara.

Shugabanin ƙasashen biyu "sun yi magana kan buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro...domin shawo kan barazanar da ake fuskanta a halin yanzu," in ji sanarwar ta Nijar, wadda aka karanta a gidan rediyon gwamnatin ƙasar.

'Dabarun haɗin kai'

Har ila yau, sun tattauna "ayyukan don haɗin gwiwar ɓangarori da dama da na duniya," in ji sanarwar, ba tare da ba da ƙarin bayani ba kan hakan.