Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya tabbatar da zaÉ“en Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na Æ™asa.
An zaÉ“i Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal É—in Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin Æ™asar.
Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan ƙusoshin jam'iyyar da suka halarci taron kwamitin zartarwar APC na ranar Alhamis.
Haka zalika, kwamitin zartarwar ya tabbatar da Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.
0 Comments