SHIMFIDA
.S.Y.
Kaduna Press
©3/8/2023
A Cikin wata katafariyar makaranta mai suna Kulliyatu Nurul Islam wadda ke titin Wunti daura da shatalctalen kasuwar Laushi a cikin garin Bauchi, Makarantar tana dauke da azuzuwan da sun kai ashirin, ga ofishin Malamai, ga na
Shugaban makaranta, ga makeken dakin taro mai cin mutane masu yawa, sai dakin bincike na Hukumar makarantar. Har ita yau tana da kawataccen masallaci, wanda daga nesa ana iya hango hasumiyarsa
mai dauke da wata da tauraro. An 'kawata makarantar da shuke-shuke masu ban sha'awa.
Yayin da makarantar take dauke da sashe-sashe. A kwai bangaren haddar Alkur'ani mai girma da sashen firamare da kuma Wurin renon yara (nursery) da bangaren babbar makaranta wato (Higher Islam). Sau tari makarantar ce take zuwa na daya a wajen musabakar Alkur'ani mai girma da akan yi duk shekara. Saboda haka ne gwamnatin jiha take ji da makarantar. Haka kuma idan wajen munakasha (muhawara) ne makarantar ce ke Zuwa na daya. Kai wannan makaranta ta bai tsaya a garin Bauchi kadai ba har ma da kasa baki daya saboda an taba zuwa gasar
musabakar Alkur'ani mai girma ta kasa da kasa ta duniya bangaren mata wadda kasar Dubai ta dauki nauyin gudanarwa. Sai ya zamanto daliban wannan makaranta ne suka ci gasar. A dalilin haka Najeriya ce ta zo ta daya, kuma daliban suka dawo gida cikin dimbin nasara tare da kyaututtuka masu tarin yawa.
Duk inda daliban wannan makaranta suke za ka gan su sun fita daban da sauran takwarorinsu na sauran makarantu saboda
yadda tsarin koyarwar makarantar ke gudana.
Wadannan nasarori da wannan makaranta ke samu. ya samo asalı ne daga wata hazikar Malama, wadda ke da matsayin Mataimakiyar Shugabar makarantar mai suna Malama Fadimatu Yahaya, wadda
ta tsaya tsayin daka don ganin daliban makarantar sun sami Nagartaccen ilimi da Nagartaceiyar tarbiyya. Wannan namijin
kokari nata shi ya jawo mata farin jini wajen hukumar makarantar da dalibai, kai har da wajen makarantar. Duk inda ake maganar karatu da makaranta ita ce kawai za kaji ana yabo tare jinjina mata.
Sannan kyawawan halayenta da dabi'unta na gari su suka yi ado ta zamo abin koyi ga dakibanta. Kuma abar sha'awa da girmamawa, ba kwai dalibai ba, kai har da Malamai suna alfahari da Ita.
.S.Y.
Kaduna Press
©3/8/2023
0 Comments