Wani abin mamaki kuma da ke damun daliban da aboka aikinta duk lokacin da take magana da harshen Labarbci kai kace
tamkar karatunta da koyarwanta duk a Saudiyya ne ta yi. Haka idan tana Turanci sai ta rikide ta dawo tamkar a turai ta kaya. Abin da ya fi ba kowa mamaki shi ne Hausarta, da kaji ba sai ma an Fada
maka ba za ka gane ba Bahaushiya bace.
Nasakorin da wannan makaranta ta samu da kuma irin gagaruman daliban da suke yayewa a tsawon shekara goma, shi ya
sa suka shirya bikin cikar makarantar shekara goma da kafuwa. Wasu daga cikin daliban da aka yaye da kuma wasu daga cikin masu karatu a halin yanzu sun yi hadin gwiwa bayan shawarwarin da suka yı a tsakaninsu, suka rubuta takarda zuwa ga Malama Fadimatu Yahaya, mai dauke da neman alfarmar Malamar da ta ba su tarıhinta a ranar da za a gudanar da wannan taro. Ta amsa wa daliban da cewa: labarin ba zai ba du a yadda suke bukata ba. Sai dai ta anminee musu da su same ta a gida. Ta ba su ranar Juma'a mai zuwa. Daliban suka yi tattaki zuwa gidan Malamar da ke unguwar Makama. Malamar ta karbé su hannu bibbiyu ta jagorance su zuwa dakin shakatawarta mai dauke da dankara-dankaran kujerun alfarmar da aka kewaye dakin da su gwanin sha'awa. Ga wani katon wurin mai dauke da littattafai. Kai da ganin tarin littattafan cikin dibaida, ka san ka zo gidan masu abin, kura da kallabin kitse. Daga gaba kuma wani katon wurin aje kayan wuta. Daga saman dakin gaba daya an kawata shi da manya-manyan hotunan addu'o'i tare da hotunan ayoyin Alkur'ani mai tsarki wadanda aka kawata su da ruwan zaiba.
Bayan dalıban sun zazzauna, su goma sha daya, an kawo musu kayan motsa baki. Malamar ta zo ta zauna ta fuskance su
cikin natsuwa. Malamar tana daure ne da atamfa super waz koriyya shar. Tana sanye kuma da sarkar Zinare da yan kunnensa sai walkiya take yi. Sabanin yadda suka saba ganin ta a makaranta cikin dogon Hijabi har kasa. Su kuwa daliban sai wancan ya kalli wannan, wancan ya kalli wannan, suna mamaki a cikin kansu na
kyan Malamar da a makaranta Hijabi yake boye da shi. Ta fara da Sallama....
Wannan Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a
Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...
.S.Y.
Kaduna Press
©4/8/2023
0 Comments