Hukumomin Senegal sun tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu biyar bayan wasu mahara sun cilla wa motar da fasinjojin ke ciki wutar a ci bal-bal.

Ministan Cikin Gidan Senegal Antoine Felix Abdoulaye Diome wanda ya bayyana lamarin cikin wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na intanet, ya ce wasu mahara ne suka yi wa motar safar dirar mikiya da yammaci Talata tare da jefa aci bal-bal cikin motar. 

Motar bas din na kan hanyarta ne ta zuwa birnin Dakar, yayin da wani gungun mutane ya tare ta. 

Direban motar Abdoulaye Diop wanda ke cikin wadanda suka jikkata sakamakon harin, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na  AFP cewa, 7 daga cikin matasan da suka rufe fuskokinsu sun kutsa har cikin bas din, inda daya daga cikinsu ya cinna wutar aci bal-bal.

A cewar Ministan Cikin Gidan, baya ga kashe mutane 2 da jikkata wasu 5, maharan sun kuma yi wa fasinjojin fashin kudi da wayoyin hannu.

Manajan kamfanin sufurin Mbaye Amar ya daura alhakin harin kan masu zanga-zangar goyon bayan jigon adawar kasar Ousman Sonko. 

Sai dai ministan ya bayyana harin a matsayin na  ta'addanci, ba tare da danganta hakan da masu zanga-zangar ba.