A yau laraba 2/8/2023 gamayyar kungiyoyin kwadago na Najeriya sun fara wata zanga-zangar a wasu sassa na kasar don nuna rashin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi har ma da wasu manufofin gwamnatin da suka jefa al’umma cikin wani yanayi na tsadar rayuwa, da kuma hauhawar farashin kayayyaki waÉ—anda cire tallafin man fetur ya haddasa.
A ranar Litinin da ta gabata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ta talbijin ga al'ummar Najeriya, inda a ciki ya jajanta wa 'yan ƙasar game da halin matsi da matakin janye tallafin mai ya jefa su, amma ya ce babu wani zaɓin da gwamnati sa take da shi da ya fi hakan.
Wakilin kd-Press: ya tattauna da wasu da ga cikin ‘yan Najeriya da suka bayyana ra’ayoyinsu sun nuna rashin jin dadin su da wannan yanayi mai wahala da yan kasa ke fama da shi.
A yayin gudanar da zanga-zangaar, shugaban kungiyar NLC Joe Ajaero Yace: babu gudu babu ja da baya a game da zanga-zangar.
Mazu zanga-zangar suna tafe ne suna maci tare da rera waka da rubuce-rubuce."A bar talakan Najeriya ya shaƙi iska,".
Kd-Press
©2/8/2023
0 Comments