A lokacin da muke makaranta ajinmu na karshe muna jarabawa, wata rana muna hira da kawata Haulatu, nake ce mata ina son na shiga Musulunci. Ta kalle ni cikin mamaki. Ai ban san lokacin da ta rungume ni ba saboda jin dadin abin da na gaya mata. Ta ce za ta gaya wa babanta. Na kalle ta cikin tsoro, "don Allah kada ki gaya ma kowa." Na fada mata fargabar abin da zai biyo baya daga 'yan uwana idan labarin ya fito, amma na ce mu tsara yadda za ta rika karantar da ni menene Islam, ita kuwa ta amince.
Amma ina yawan tambayar ta dangane da wadansu abubuwa addinin Musulunci. Kullum muka fita wajen tara. hirarmu kenan. Safiyar Litinin na zo makaranta ban ga Haulatu ba, duk hankalina ya tashi ina ta tunani har yanzu ba ta bullo ba. Ko lafiya? Zuwa can sai na hango ta. Da tasowarta, sai na ga jikinta duk ya yi sanyi. idanunta sun kada sun yi ja. Sai na tashi da sauri na riko hannayenta, "Yaya dai mutuniyar? Ta girgiza kanta tare da cewa an yi wa mahai finta sauyin gurin aiki zuwa Abuja. Ita da Hajiyarta. wato Mahaifiyarta, sai an gama jarabawa za su tafi. A nan na ce. "A gaskiya zuwa gidanmu ba zai yiwu ba saboda wasu dalilai. Na karbi littafinta na rubuta adireshin gidanmu na ba ta. "Na ce duk lokacin da muka gama jarrabawa za muje. Hakan kuwa aka yi. Ran da muka rubuta jarrabawarmu ta Karshe muka je gidan su Haulatu da ke Rimin Jahun. Muna shiga Haulatu ta ce wa Hajiyarta, "Ga Chinyarena." Na durkusa har Kasa cikin ladabi da danyar Hausata na gaishe ta.
Ta amsa mini cikin sakin fuska har na ji kunya saboda daga ni sai riga iya gwiwa, sai dan kwali a irin shigar da na saba da ita. Haulatu ta ja ni zuwa dakinta, ta dauko mana abinci da ruwan lemo. Bayan mun ci, na ce zan tafi. Ta ba ni hakuri da cewa na bari ta yi sallah. Ta je ta yiwo alwala, ta shimfida darduma. Ta dauko doguwar riga ta sanya. Ta dora hijabi a kanta. Sai wani kamshin turare yake tashi a jikin kayan. Ina daga gefe ina ganin yadda take gudanar da sallarta cikin natsuwa. Sai na ji har tsikar jikina tana tashi, na ji kamar ni ma in tashi mu yi tare. Bayan ta kammala, muka fito domin ta raka ni, Hajiyarta ta ba ni dari biyu don in hau kabu-kabu. Na ki karba
saboda sanin halin mahaifiyata. Na karbi ashirin ina godiya.
Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a
Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...
.S.Y.
Kaduna Press
©18/8/2023
0 Comments