.S.Y.
Kaduna Press
©11/8/2023
Nikuma da kawata mai suna Esther muka dauki littafinmu domin bitar darasin da ya gabata, kafin Malamin ya shigo. Can sai
ga Malamin namu ya shigo kamar an jefo shi daga sama. Ya daka tsawa: "Lafiyarku ku kuwa! Kun cika mana makaranta da surutu, (kamar kasuwar baje-koli)." Ya umurci gaba đayan ajin damu tashi
tsaye. Bayan mun mike tsaye ya dauko wata sharbcbiyar dorina a ofishin Malamai, ya tambayi Shugaban daliban ajinmu da ya nuna masa wadanda suka yi surutu. Budan bakinsa ke da wuya sai ya
"Gaba daya ajin babu wvanda bai yi surutu ba. Na daga hannu sama. "Malam a gaskiya mu biyu ba mu yi surutu ba." Na nuna Esther da muke tare. Gaba daya 'yan ajin kamar sun hade mana baki suka ce:
"Malam sun yi, sun yi!" Sai da Malamin ya tsawata musu suka yi shiru. Tashin Mataimakiyar Shugaban daliban ajin, mai suna Haulatu Habib, wadda kujerarta a bayanmu take ta nuna mu da yatsa. "a gaskiya wadannan su biyu ne kawai ba su yi surutu ba." Malamin ya ware mu gefe guda, ya zane su gaba dayansu.
Bayan Malamin namu ya gama darasinsa ya fita, 'yan ajin gaba daya suka taso wa Haulatu kamar za su cinye ta danya. Suna
ta tuhumar ta dalilin da ya sa ta ce ba mu yi surutu ba. Ta ce musu ita gaskiya ta fada. Tun daga sannan muka zamanto aminan juna da Haulatu Habib.
Ina lura da dabi'un Hausawa, maimakon abin ya fita a raina sai ya fara ba ni sha'awa, musamman ma lullubinsu. Ko da a makaranta haka zan gan su da lullubinsu lif-lif da su gwanin ban sha'awa. Na lura da yadda suke girmama Alkur'aninsu ba a taba shi sai da tsarki, yayin da mu kuma namu sabanin haka. Kuma ko da ba-haya ko fitsari suka yi sai sun yi tsarki.
A gaskiya kusan zan ce wadannan su suka fi ba ni sha'awa daga halayensu. An ce komai nasu a tsare yake a littafinsu mai tsarki, yayin da namu wasu abubuwan sai dai a hada da hikima. Duk irin sa kaya marar ma'ana da da mutanenmu ke yi
kamar damammen siket ko wando, ni ba ni sawa. Wata rana za mu je addu'a da daddare, wasu daga cikinmu sun yi irin wannan shigar, sai wadansu 'yan iska suka bi mu za su yi mana fyade. Da kyar muka sha. Wannan ya sa na bar wannan shigar kuma na kyamace ta
Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a
Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...
.S.Y.
Kaduna Press
©11/8/2023
0 Comments