.S.Y.
Kaduna Press
©10/8/2023

Asalamu alaikum wa kahmatullah wa barkatuhu. Gaba dayan daliban suka amsa da cewa "wa alaikumus salam".
Dakin an yi tsit, banda karar na'urar sanyaya daki ba ka jin komai. Malamar ta fara da "A'uzu billahi minas shaidanir rajim.
Bismillahir rahmanir rahinn. Rabbish rahli sadiri wa yassirli amnri wahlul ukdatan min lisani yafkahu kauli, wa salli ala Muhammad wa alihi wa sallim."
Asalin sunana Chinyere. Sunan Mahaifina Chibuzor. sunan mahaifiyata Ngozi. Mu asalin cikkakun. 'yan kabilar Igbo ne.
Kuma an haife ni a Karamar Hukumar Okwa South. wadda ke cikin jihar Anambra. Mahaifina ya kasance yana aiki a Ma'aikatar Railway. Tun bayan haihuwata ba su sake samun haihuwa ba. Ni kadai ce a wajen mahaifana. Na yi makarantar fiamare, ina Sakandare aji uku aka yi wa Mahaifina sauyin wurin aiki zuwa garin Bauchi. Bayan mun dawo garin Bauchi mun samu gida a Railway (quarters). Mu kadai ne a cikinsa. Gidan dan karami ne. Da ka shiga sai dakin shakatawa da dakunan bare biyu. Sai dakin girki da bayan gida.

Bayan dawowarmu aka sama mani makaranta mai suna Government Day Secondary School Kofar ldi. Bauchi. Kafin na fara zuwa makaranta sai da Mahaifiyata ta ja mini kunne: "Babu ruwanki da 'ya'yan Hausawa." Na ci gaba da zuwa makaranta. Kullum zan tafi sai an yi min gargadi. Maganar mahaifiyata na
shiga ta sosai, sai da na ji ba na son Hausa da Hausawa gaba daya.

Kullum bayan na taso daga makaranta zan dafa abinci in dauka in kai wa mahaifiyata a shagonta da ke kasuwa, shagon sai da garin rogo da manja da sauransu. Kullum sai yamma muke dawowa gida., Ba zan taba mantawa ba wata rana bayan mun shiga aji mun zauna, a lokacin darasin Turanci ne muke da shi, Malamin bai shigo ba, gaba dayan ajin ana ta surutu. Wasu daga cikin daliban Sun tashi daga gurin zamansu sun koma wani gurin daban saboda su ji dadin, surutu. An yi gungu-gungu. wasu na labarin fima-fimai. wasu na Labarin Kwallo wasu kuma Labarin Siyasa, da abun da ke faruwa a kasar mu.

Wannan Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a

Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba...

.S.Y.
Kaduna Press
©10/8/2023