KD PRESS ✍🏻
©28/July/2023
Kamar kowace shekara, a jiya Juma'a 28/7/2023 dubun dubatar ƴan'uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky (H) ne suka fito muzaharar nuna juyayi da kisan gillar da aka yiwa Jikan Mazon Allah (S) Imam Hussaini a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijira (As) a gaba daya Najeriya, suma da'irar ta kaduna sun bi sahun takwarorin su, inda suka gudanar da gagarumar Muzahar Ashura, domin nuna juyayi da Kisan Gillar da akai ma jikan Manzon Allah (saww).
Imam Husaini (as) jika ne a gurin Manzon rahama (S) wanda kafirai suka yiwa kisan gilla a irin wannan rana ta 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira a filin Karbala na ƙasar Iraqi.
Masu muzaharar sun fito ne Maza da mata Wanda aka fara daga Tsakiyar cikin garin kaduna Kano Road har zuwa kasuwan bacci.
An fara Muzaharan Lafiya an Tashi lafiya.
Ga wasu daga cikin Hotunan da muka daukar muku a wajan.
KD PRESS
©28/July/2023
0 Comments