IMAM HASSAN ALMUJTABA (A.S)

An Tambayi Imam Hassan (a.s) cewa: Ya ÆŠan Manzon Allah (s) Meyasa (Mu Mutane) muke tsoron mutuwa da gudunta?

Sai Imam Hassan (a.s) yace: "Kuna tsoron mutuwa ne domin kun lalata Lahirarku kun Gina Duniyar ku, Shiyasa kukejin tsoron a daukeku daga inda kuka gina zuwa inda kuka ɓata(Lalata)".

📖:Biharil Anwar/ vol 6/ page 129. 

A madadin Da'irar Kaduna, muke mika Sakon bangajiya, ga mahalarta taron tinawa da, haihuwar shugaban Samarin Aljanna, jikan Manzon Allah (s.a.w.w) da Khadijatul Khubra (a.s), kuma Babban ÆŠa ga Imam Ali da sayyida Zahra (a.s), kuma Babban ÆŠan uwa ga Imam Husaini da Sayyida Zainab (a.s), kuma Imami na 2 daga cikin Imaman shiriya (A.s).

Allah ka biyamana bukatunmu dan Albarkar Imam hassan (As).