Aranar Asabar 12 gawatan 12 na shekarar 2015, wandaya yi daidai da 1 ga watan Rabi'u-Auwal 1437 Hijira ne. wani abu mai kama da mafarki ya faru a Nijeriya, da misalin karfe 12 na ranar ne rundunar sojojin Nijeriya suka zo birnin Zariya da rana tsaka suka hau kisan yan Shi'a membobin 'Harka Islamiyyah' karkashin jagorancin Shaikh Ibrahim Zakzaky (H)
A lokacin wannan Ta'addanci da sojojin gwamnatin Nijeriya suka yi bisa hujjar cewa an tarewa shugabangu Majo Janar Tukur Yusuf Burtai hanya, sun,kashe dimbin almajiran Shaikh Ibrahcem Zakzaky (H) a wurare uku da suka datse suka killace, wato Hussainiyyah Biqiyyatullah' da ke No: 1 kan titin Sokoto Road, da gidan
jagoran 'Harka Islamiyyah Shaikh Zakzaky (H) da ke unguwar Gyallesu a cikin birnin Zariya, da kuma 'Darur-Rahma' wanda aka fisani da makabartar Shahidai ko 'Film Village' da ke kusa da kauyen Dembo a bayan garin Zariya.
A wannan kashe-kashen ta'addanci da rundunar sojojin Nijeriya suka aiwatar cikin kwana biyu yiņi uku (Asabar zuwa Litinin), Sun kashe kusan mutum Dubu maza da mata da kananan yará, wanda ba su dauke da makami sai carbi da Hailala da Kabbara da suke yi.
Sun kashe dimbin matan aure wasunsu ma da juna biyu ko-yau-ko-gobe, kuma sun kashe yan mata kusan wadanda suke karatu a makarantun Sakandare da Jimi'o'i
daban-daban. Sun kashe tsofaftfi'yan sama da shekaru 70 da haihuwa, kuma sun kashe dimbin mataÅŸan da ke karatun digiri ajami'o'i da dama na ciki da wajen Nijeriya.
Ta kai ga sun kashe iyali baki dayansu (mata da miji da'yarsu), kamar kuma yadda suka kashe wa wani uba
'ya'yansa hudu dukkaninsu yan Jami'a, haka nan kuma sun kashe wa wata uwa ya'yanta biyar dukkaninsu yan Jami'a, sun ma kashewa wani bawan Allah hazikan 'ya'yansa mata guda uku da kuma jikarsa da surukinsa, suka kashe wa wata
baiwar Allah ya'yanta shida da mijinta da wasu yan uwanta.
A lokacin wannan ta'addanci, saboda tsabar harbin kan mai uwa da wabi da sojoji ke yi, nan take wata mata mai
ciki ta haihu saboda firgici, suka cimmata suka harbeta kuma suka harbe jaririn da ta Haifa shi ma ya yi Shahada ba tare da ya sha nonon mahaifiyarsa ba!
Suka harbawa gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) gurneti ya kama da wuta, suka shiga gidan suka rika harbin mutane suna jefa su cikin wuta suna konewa alhali
da ransu, majinyatan da ke kwance a gidan Harisawa da ke jikin gidan Shaikh Zakzaky, suka zuba masu Fetur suka
kunna masu wuta suka kone kurmus!
A wannan waki'a an rasa manya-manyan Malamai almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) irinsu Shaikh Muhammad Turi Kano, Shaikh Mukhtar Sahabi Kaduna,
Shaikh Mustapha Lawal Potiskum, Malam Muhammad Kabir Al-Kanawy, Malam Muhammad Auwal lyal Zariya, da irinsu Dokta Mustapha Sa'id, Malam Ibrahim
Usman da sauransu.
Sun kashe 'ya'yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) guda uku dukkaninsu maza, tattare da cewa shekara guda baya ma sun kashe wasu ukun wadanda duk suna karatu ne a jimi'o'in kasashen waje, sannan suka kashe dan wan Shaikh Zakzaky mai suna Shamsuddeen, sannan suka
kashe yayar Shaikh Zakzaky mai suna Goggo Fatimah, suka jefa ta cikin wuta ta kone kurmus!
Sun isa ga Shaikh Zakzaky (H) da iyalansa da ke fake a wani karamin daki dakin, suka bude musu wuta, inda suka harbi matarsa Malama Zeenatuddeen a wurare da dama a jikinta, suka harbi Shaikh Zakzaky (H) a wuraren kisa a jikinsa, suka kashe ragowar wadanda ke tare da shi face yan matan da Allah ya tseratar.
Suka kama dimbin mata da 'yan mata da matan aure, suka kai su barikin sojoji suka rinka wulakanta su suna cire musu Hijabi, suka rinka jika su da ruwan sanyi suna musu izgilanci iri-iri! Suka wulakanta gawarwakin mutanen da suka kashe, suka ba mutanen gari damar sace wayoyi da Zobba da kudaden da ke aljifan gawarwakin!
Sun kashe mutane a shingayen binciken da suka kakkafa a duk mashigar Zariya, duk wani mutum da suka gani sanye da bakaken tufafi sukan sauke shi su bindige shi. A irin haka sun kashe mutanen da ba 'yan'Harka Islamiyyah' ba da dama.
Suka kama daruruwan almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka kai su bariki suka rinka yi musu gwale-gwale suna azabtar da su, wadanda ke da raunuka na
harbin harsashi suka ki su kai su asibiti, suka wuce da su kurkukun Kaduna kai tsaye aka ci gaba da tsare su ba tare
da shari'a ba!
Bayan sun gama kisan, sai suka kwashe wasu daga cikin gawarwakin, suka je unguwar Mando da ke bayan garin
Kaduna, suka haka katon rami suka zuba maza da mata yara da manya suka bisne su a kabari daya, ba tare da yi masu Wanka ko Sallah ko sanya masu Likkafani ba, hasali ma wasu da sauran ransu suna motsi suka bisne su! Sannan
suka kwashi wasu daruruwan gawarwaki suka je wasu dazuka da ke karkashin ikonsu suka bisne su, wanda zuwa yanzu ba a iya gano wuraren ba (ko in ce: bani da masaniya na in da suka kai su).
Sun raunata daruruwan yan uwa almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) da raunuka daban-daban, ta kai a sai da aka fita da wasu kasashen waje don Jinya, wasu sun rasa sassa na gabobin jikinsu, wasu kusan gaba dayan fafar jikinsu ta kone, wasu kuma sun samu nakasa a wasu sassan jikinsu.
Awannan ta'addanci na sojoji, sun kashe kusan mutum dubu. Sun maida kusan mata 550 Zawarawa. Sun maida yara sama da 1300 Marayu. Sun sa dangi da iyaye sama da 4000 cikin garari, kewa da kadaici. Sun durkusar da iyaye dadama saboda kashe musu masu taimakonsu.
Duk wannan ta'addanci bai ishi sojojin ba, sai da suka sa Gireda suka rusa gidan Shaikh Zakzaky (H) suka kwashe
kasar gidan suka maishe da filin gidan wajan hányar wucewa! Suka harbawa 'Hussainiyyah Baqiyatullah Gurneti suka ruso da ita akan mutanen da suka nemi
mafaka a cikinta, sannan suka sa Katafila suka rusheta gaba daya!
Suka je Darur-Rahma' suka ruguza duk gine-ginen gargajiya na miliyoyin Naira da ke wajan, suka lalata duk wasu kayan Tarihi na tunawa da Shehu Usman dan Fodiyo da ke wajan, suka ruguza gine-gine a kan kaburburan Shahidai da ke wajan, suka maida rayayyen wurin ya zamo tamkar kufayi! Sojojin Nijeriya da taimakon gwamnatin jahar Kaduna ba su dakata a nan ba, sai da suka je makwanci, wato
Hubbaren mahaifiyar Shaikh Zakzaky (H) "Hajiya Salaha Hari Jamo Cemetry da ke unguwar Jushi a cikin.birninvZariya, suka ruguza Hubbaren baki dayansa. Suka wuce Fudiyyah Islamic Center (F.l.C) Zariya suka ruguzata, suka ruso da gine-gine akan littattafan addini da muhimman kayayyakin da ko ajiye a wurin, suka ba yan kallo damar sace kayayakin da suke bukata a wurin.
Duk jerin wadannan abubuwa da muka kawo, sun faru ne cikin mako guda kacal,
wato daga ranar 12 ga watan 12 na shekarar 2015, zuwa ranar 17 ga watan 12 na shekarar 2015
0 Comments