Kaduna Press
©12/12/2022

Hakika almarin waki'ar zariya mai daci a zuciya da sosa rai, abu ne da alkalami✍🏼 ba zai gaji da rubutawa ba, kuma tari zai sajjala shi har kiyama ba za a manta da barnar da sojojin Najeria sukayi ba.Na kashe daruruwan ‘yan kasa fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da kuma jikkata da dama a cikin kwanaki biyu kacal, 12-14 ga watan Disamba, 2015. Karkashin jagorancin tsohon Hafsan-Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai Bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Hakika wannan kisan kiyashi da aka yi wa al'ummar Musulmi ‘yan Shi’a ba lamari ba ne wanda ya shafi Najeriya kadai ba. Batu na kisan kiyashi a kan al’umma lamari ne wanda ya shafi dukkanin mai Imani (Humanity) dama Kasashen duniya. Don haka muna kira ga Kasashe mambobin Majalisar dinkin duniya da su tuhumi Najeriya kuma su hukunta ta dangane da wannan kisan kiyashi da ta aikata, kar su bar kasar ta sha daga wannan mummunan laifi.

Hatta Hukumar Bincike (J.S.I) ta jeka-na-yi-ka da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa ta tabbatar da yi wa gawawwakin ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) akalla guda 347 Kabari na bai-daya, wadanda Sojojin Najeriya suka kashe kuma suka binne su tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kaduna bisa umurnin Gwamnan Jihar ta Kaduna, Nasiru Elrufa’i.

Ya kamata ne Majalisar Dinkin Duniya ta cire tarayyar Najeriya daga kasancewa cikin mambobin Kasashen kawancenta bisa Kudiri na 6 cikin dokokin kudurinta (Article 6 of the United Nations charter). Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) ya kamata ya gurfanar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mukarrabansa a wannan aika-aika irin su tsohon Hafsan-Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru Elrufa’i a gaban mai gabatar da kara na Kotun manyan laifuka ta duniya, domin tuhumar su a kan aikata laifin kisan kiyashi.

Ya kuma kamata Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) ta haramta sayar wa da gwamnatin Najeriya Makamai na yaki bisa kudiri na VII na dokokin Majalisar har sai an gudanar da bincike na hakika mai zaman kansa dangane da kisan kiyashi da aka yi a garin Zariya da kuma bayyana masu laifi tare kuma da hukunta su. Daukar wannan mataki a kan Najeriya zai taimaki Majalisar Dinkin Duniya ta fuskoki guda biyu kamar haka: (1) “Samar da yanayi wanda zai sabbaba yin adalci da kuma kiyaye dokoki na Kasa da kasa.” (2) “Daukaka da kuma tabbatar da mutunta hakkin bil’adama tare kuma da tabbatar da ‘yancin dan’adam na rayuwa ba tare da wata tsangwama ba a kan sha’anin addini.”

Hakazalika, duk da za a zargi Majalisar Dinkin Duniya dangane da kin yin magana a kan lamarin Kisan kare dangi da aka yi a garin Zariya, to lallai kuwa shirun ‘yan majalisar tarayyar Najeriya da ke Abuja shi ne mafi muni. A Shekar data gabata ne aka yi rahoton kwakwazo da kuma Allah wadai da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi dangane da yunkurin Sojojin Najeriya na sanya Kungiyar IPOB cikin jerin Kungiyoyin ‘yan ta’adda. Tabbas mun yi matukar mamaki, ina Bukola Saraki yake a lokacin da Sojojin Najeriya suka aikata mafi munin laifi a kan Musulmi ‘yan Shi’a a cikin watan Disambar shekarar 2015?

Ina Bukola Saraki yake a lokacin da Sojojin Najeriya suka kashe sama da mutum dubu daya a garin Zariya tsakanin ranekun 12-14 ga watan Disamba, 2015? Ina Bukola Saraki yake a lokacin da Elrufa’i ya haramta Harkar Musulunci a Najeriya, ya kuma dukufa wajen daukar dawainiyar
zauna-gari-banza da jami’an tsaro domin murkushe ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya, ta fuskacin kisa, jikkatawa, konawa da wuta da kuma rusa masu gine-gine?

Ina Bukola Sarki yake a lokacin da gamayyar jami’an tsaro wadanda suka hada da, Sojoji, ‘yan sanda da kuma jami’an tsaro na farin kaya suka kaddamar da kisa na haka-siddan a kan Musulmi ‘yan Shi’a a garin Funtuwa, Kaduna, Jos dama sauran garuruwa a cikin watan Oktoba na shekarar 2016? Shin Bukola Saraki ba ya Kasar ne a lokacin da jami’an tsaro ‘yan Sanda suka kashe sama da mutum talatin a garin Kano a yayin tattakin Yaumul Arba’een a cikin watan Nuwambar shekarar 2016?

Wannan da ma sauran wadansu abubuwa sun isa su gaskata cewa akwai makirci na yin shiru tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kuma jami’an gwamnatin Najeriya dangane da musgunawa da cutarwa, hade da zaluncin da ake yi wa ‘yan uwa Musulmi na IMN. Shakka babu, wannan ba zai dakile mu ba a kan fafutukarmu wajen ganin an yi adalci dangane da kisan kiyashi da aka yi a garin Zariya. Don haka muna kara jaddada bukatarmu ta a gaggauta sakin Pasfo din Jagoranmu , Shaikh Ibraheem Zakzaky, da mai dakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Isiya-.S.Y.
A Madadin 
Kaduna Press
©12/12/2022