Gwamnatin Kaduna Taki Bin Umarnin Kotu
KADUNA PRESS.

Tun a shekarar dubu biyu da sha bakwai (2017) ne dai al'ummar kasuwar bacci suka garzaya kotu domin gabatar da kararrakin su, kan hana gwamnatin jihar Kaduna rushe kasuwar,

Amma sai a karshen watan da ya gabata ne Babbar kotun jihar Kadunan karkashin Mai shari’a Edward Andow ta umarci gwamnatin jihar da ta mayarwa da 'yan kasuwar ta bacci shagunan su da ta rusa, tare da biyan su diyya.

Kusan wata daya kenan da yanke wannan hukunci amma gwamnatin jihar ba ta ce komai ba dangane da lamarin.

Alhaji abdullahi kaya-kaya shugaban kungiyar masu shaguna a kasuwar ta bacci ya shaidawa manema labarai cewa a kalla akwai shaguna kusan 4600 daga cikin kasuwar zuwa 'yan raga, mune da kudaden mu muka gina shagunan mu. kuma babu abin da bama biyan gwamnati, rabano da duk abinda kasan ana biya! Inji shi.

Wani lauya mai zaman kansa (Bar. Al-Zubair Abubakar) yace aidama kasuwanni irin wadannan ba'a karkashin kulawar gwamnatin jiha suke ba, suna kulawar kananan hukumomine, amma jiha tayiwa mutane karfa-karfa, to abinda kotu ta tabbatarwa da gwamnatin jihar kenan.
©KD press.
-26102022.