Ta’addanci Ya Zama Tarihi, Nijeriya Na Cikin Aminci – Lai Muhammad
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad, ya ce babban kalubalen ta’addanci a Nijeriya ya kare idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro.
Mr. Lai ya bayyana haka ne a wani zama na ministoci a taron makon wayar da kan jama’a da kungiyar UNESCO ke shirya wa.
Ya kara da cewa, sojoji da sauran jami’an tsaro sun jajirce wajen kare dukiyoyi da rayukan ‘yan Nijeriya da wadanda ba ‘yan kasa ba.
Ya ce, “Zan iya tabbatar wa, duk sojojinmu da sauran jami’an tsaro suna yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro da kare ‘yan Nijeriya da baki da ke zaune a Nijeriya.
“An ragargaji ‘yan ta’addan. An tarwatsa maboyarsu. A yau kasarmu ta fi kowane lokaci zaman lafiya in akayi la’akari da baya-bayan nan, sabida sadaukarwar da jami’an tsaron mu, maza da mata suka yi.
©KD press.
-26102022.
0 Comments