-KADUNA PRESS✍️.
Dubun-dubatar 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzaky na yankin Kaduna da kewaye suka fito domin gudanar da tattakin tunawa da ranar arba'en din kashe jikan Manzon Allah (S) wato Imam Hussani, da aka kashe ranar goma ga watan Almuharram shkara ta sittin bayan hijira.
Da asubahin fari ne dai Hoton Sheikh Zakzaky ya bayyana a babbar gadar dake kawo ta hanyar shiga ko fita daga cikin birin Kaduna, wanda hakan ke nuna alamun cewa 'yan uwa musulmin na Kaduna sun gudanar da tattakin a wannan shekarar kamar yadda suka saba gabatarwa duk shekara.
Wakin yan uwa Musulmi na yanki jaduna Sheikh Aliyu Umar (Tirmidhiy) ne ya jagoranci tattakin, kuma yayi takaitaccen bayani akan makasudin fitowar su domin gudanar da shi wannan tattaki din.
A yayin zantawar sa da manema labarai Malam Tirmidhiy yace: lallai wannan tattakin ba iyakacin yan Shi'a ko al'ummar musulmi ne ya kamata su ringa gudanar dashi ba, Idan ka duba lamarin Imam Hussani zakaga cewa ba iyakacin maganar addini bane a'a harda abinda ya shafi 'yan adamtaka,
A yayin da Imam Hussani ya karaso filin Karbala tarihi ya tabbatar mana da cewa: harda kirista a mutanen sa, harda mata da kananan yara, to kaga mutum baida wani cikakken uzuri, inji shi.
Bayan shiga cikin garin Zaria ne dai wakilin 'yan uwa musulmin na garin Zaria Malam Abdulhamid Bello ya tarbi tattakin.! inji wakilin mu dake gurin.
Tattakin dai ya gudana cikin luma da tsari kamar yadda suka saba gabatarwa idan jami'an tsaro basu farmaki mahalartan ba.
Mahalartan dai suna tafe suna rera wakokin juyayi da nuna alhini a bisa abinda ya samu jikan Manzon Allah Imam Hussani da mutanen sa a wancan lokacin.
Malam Aliyu Tirmidhiy yayi jawabi a gurin rufewa inda ya bayyanawa cewa: lallai kamar yadda aka sanmu da tsari da kuma binshi, to mu kasamce a hakan, kowa yabi inda ya dace domin komawa gida, idan kuma sunzo (jami'an tsaro) kafin mu kammala to muna fatan Allah ya bamu sabati da juriya, inji shehin Malamin.
Bayan ya kammala sai Malam Abdulhamid Bello ya dora nasa jawabin, inda yayi bayani takaitaccen akan yanda za'a gudanar da tattakin na gobe juma'a, da kuma wanda zai gudana a cikin birnin Abuja.
'Yan uwa musulmin sun rufe tattakin ne a makabartar dake Unguwan Bashar ta cikin Zaria city.
Akayi Addu'a aka sallami kowa.
@KD-press.
©-15092022.
0 Comments