AN GUDANAR DA GASAR FARETIN MAKARANTUN ISLAMIYYU A GARIN KADUNA.
A yau asabar 22/10/2022 aka shirya domin gabatar da gasar faretin makarantun Islamiyyu na cikin garin Kaduna da aka saba shiryawa duk shekara domin girmamawa ga Fiyayyen Halitta Ma'aiki (S), da kuma murna da zagayowar watan da aka haife Shi (S).
Kamar yadda suka saba gabatar da wannan taro almajiran Sheikh Zakzakiy a bana ma basuyi kasa a gwuiwa ba.
A bana makarantun Islamiyyun sun fara zagayen ne daga bus top na hayin rigasa da misalin karfe goma na safiya, suka biyo titin dake fitowa bakin ruwa, suka dauke layin titin lokoja (layin Jabir Khamis), aka rufe zagayen a layin Shanono (inda aka gudanar da gasar faretin),
A yayin gudanar da zagayen wakilanmu sun zanta da wasu mahalarta zagayen, da kuma masu kallon zagayen.
Lallai munji dadi sosan gaske da kawo mana wannan zagaye na mauludi unguwar mu, domin a yanda na fahimta an dade ana yin wannan zagayen wannan ne Allah yasa aka kawo shi hayin mu!! Cewar wani dan kallo.
Gaskiyar magana wannan zagayen ba iyakacin 'yan Shi'a ne ya kamata ace sunyi ba, kamata yayi ace dukkan al'ummar musuilmi su fito domin nunawa Ma'aiki (S) so da kauna! Inji wata 'yar kallo a gurin zagayen.
Kamar yanda kowa ya sani cewa wannan zagayen ba iyakacin namu bane, a'a na kowa-da-kowa ne, domin Annabin rahama ne ga kowa, musulmi da wanda ba musulmi ba, inka lura mukan gabatar da taruka irin wadannan tare da ahalul kitabi (kirista), sannan da ko wanne bangare na akidun Musulumci. Inji wani daga cikin masu zagayen.
A dai-dai karfe biyu da mintuna (bayan sallar azahar) aka fara gabatar da makarantun domin gudanar da faretin nasu.
A lokacin da karfe hudu ta doso, misalin karfe 03:45 aka tafi hutu domin gabatar da sallar la'asar da kuma cin abinci.
Ana kammalawa aka dawo domin dorawa daga inda aka tsaya.
Haka aka dinga zayyano makarantun daya-bayan-daya, har aka zo ta karshe.
Bayan kammala faretin nasu ne wakilin 'yan uwa na garin Kaduna da kewaye Sheikh Aliyu Tirmidhiy yayi takaitaccen jawabi.
Inda Malamin ya maida hankali kacokaf kan abin da ya shafi karatun yara kananu da kuma kara nuna musu girma da darajar Ma'aiki (S) musamman a makarantu da kuma gidajen iyayen su.
Shehin Malamin yayi bayani kan wajabcin biyawa yara kudin makaranta dake kan iyayen su, domin Allah yayi nuni akan kubutar dasu (iyali) daga wutar jahannama.
Bayan nan ne wadanda ke kula da lamarin fareti da gasar musabaka da aka gabatar a satin da ya gabata (inji wakilinmu), suka amshi abin magana domin bayyana wadanda suka cinye gasoshin na fareti da musabakar,
Bayan kammala baiwa 'yan musabaka kyautukansu na abubuwan da suka samu a musabakar.
Madaratu Ahlul Baitir Rasul miyatti Allah ne suka lashe na daya a bangaren wake.
Madarasatu Imam Sadik nasarawa sukaci na biyu a waken.
Madarasatu Ikamatud Deenil Islam na uku a waken.
A bangaren kwalliya kuwa (dressing) Madarasatu Ahlu Baitir Rasul na daya.
Madarasatul Fudiyya U/Rimi ta biyu.
Madarasatu Ikamatud Deenil Islam ta uku.
A fareti kuwa Madarasatul Fudiyya U/Rimi tayi na daya.
Madarasatu Ahlul Bait tayi na biyu.
Madarasatul Fudiyya U/Ma'azu tayi na uku.
An dai fara lafiya kuma anyi lafiya an kammala lami-lafiya kowa na murna yana nishadi, akayi addu'a aka sallami kowa da kowa.
©KD-press.
-22102022.
0 Comments