A cikin takaitaccen jawaban sa da ya gabatar jim kadan bayan kammala zaman Makokin Ashura a jiya Lahadi 7.8/2022 a U/Rimi Kaduna, wakilin 'yan'uwa na Kaduna da kewaye, Malam Aliyu Turmizi ya yi kira ga daukakin 'yan'uwa na Kaduna da su kasance cikin tsari kamar yadda aka sansu a yayin Muzaharar Ashura ta na wannan shekara 2022, wanda za a gabatar Idan yanayi ya bada dama.
Ya ce, "Babu shakka za mu yi Muzaharar Ashura, kuma sako muke Isarwa ga Al'ummah da raya wannan Addini. Amma abun bukata shine kowa ya kasance cikin tsari, kuma kar da kashiga aikin da ba a saka ka ba, zamu daukin mataki a kan dun Wanda yaki bin tsari.
Malam ya kara da cewa, "Zuwa yanzu dai kowa ya ji irin dasisar da makiya Addini suke kullawa musamman a garin Kadunan nan, don haka kasancewar ka dan'uwa a cikin tsari shi zai rusa shirin makiya a kanka. Ya bayyana cewa, kada dan'uwa ya shiga aikin da ba a sa shi ba. Duk aikin da 'yan'uwa suga wasu ba'adin 'yan'uwa na yi, an sa su ne. Kuma bin wannan tsari to shi ne bin Jagora da hakikanin Addini."
Muna rokon Allah ya maida musu dukkan mummunar abinda suka kulla zuwa kansu alfarmar alfarmar Imam Hussain (AS).
Kaduna Press
8/8/2022
0 Comments