Yau Alhamis 4/8/2022-6/1/1444H Ana cigaba da Zaman Makokin Jikan Manzon Allah (S) Imam Hussain (As) a Da'irar Kaduna. Kamar kullum yau Malam Jamila Auwal (Muktar Sahabi Kaduna) ce ta gabatar da jawabi, Malam ta gabatar da jawabi ne game da shaksiyar Sayyida Zainab (S.A) da Musa'ib (musibar) da ta fusakanta a rayuwar ta bayan wafatin Manzon Allah (As), da Mahaifan ta, Sannan Malama ta bayyana cewa: Sayyida Zainab ta kasance kamar Mahaifiyarta. Ta kara da cewa: Sayyids Zainab SanfuriCe (Abin koyi) ga dukkan nin Mata. Sannan a wannan zamanin yan uwa Mata na da Zainab abin koyi wato Malam Zeenat Ibrahim Zakzaky, Sayyida Zainab a waki'ar Karbala, Malam Zeenat ta bayar da 'ya'yanta Shida (6) a wannan Addinin. Ta cigaba da cewa: duk wanda ya samu kanSa a gyallesu zai iya fahimtar kwatan kwacin Musifar da ta fuskanta a Karbala.
Bayan Malam ta kammala sai a ka mika abun magana ga wakilin yan uwa na Da'irar Kaduna, Malam Aliyu Umar (Tirmizi) Malam ya dan yi Karin bayani game da jawabin Malama, in da ya bayyana cewa wani wani marubuci ya na cewa: ba dan da Sayyida Zainab ba, da Karbala bata cika ba, Imam Hussain (As) ya fuskanci makiya da karfin ruhinSa da takobi, Ita kuma Sayyida ta fuskanci makiya ne da karfin ruhinta da kuma bakinta, hakazalika ta ba da gudunmuwa mai yawan gaske a wannan Addinin, abar koyi CE ga kowa musamman ma Sisters.
Daga karshe Sha'irai sun gabatar da wakoki na juyiyi da tunatar da mutane waki’ar Asura da shahahar iyalan Manzon Allah cikin wake. Bayan sun kammala akayi Addu'ah a ka sallami kowa.
KUBIMU TA SHAFUFFUKAN MU MA NA DANDALOLIN SADARWA (SOCIAL MEDIA)
WEBSITE, FACEBOOK, TWITTER, TELEGRAM, INSTAGRAM, YOUTUBE, WHATSAPP, AUDIOMACK.
@Kd-Press
Kaduna Press
©4/8/2022 -6/1/1444H
0 Comments