Idan mutum ya bibiyi tarihin wannan waki’ar ta Karbala, tun daga farkonta har karshenta zai ga cewa mata sun ba da gudummuwa mai yawan gaske a ciki. Kuma wannan gudummuwar tasu ta wanzu har yazuwa wannan zamani namu, kuma za ta ci gaba da wanzuwa.
Alal misali zaman makoki wanda ya zama wata zaunanniyar Sunna tun bayan Shahadar su Imam Husain (AS) wadanda suka soma yin wannan zaman makoki sune matan da suka yi masharaka a cikin wannan waki’ar ta Ashura, wato su Zainab (AS) sun soma yin haka a Sham da kuma bayan isar su Madina kamar yadda za mu ga haka a nan gaba insha Allah.
Haka nan sa bakaken kaya a irin wannan zama na makoki su suka soma yi. Wannan ya auku a Madina har ma ya zo akan cewa idan suna wannan zaman makoki Imam Zainul Abidin yakan sa a yi abinci a kai masu, kuma daga nan Malaman Imamiyyah suka tafi a kan Sunnah din sa bakaken kaya a lokacin makoki, domin kamar yadda aka sani Sunnah ita ce fadin Ma’asum ko aikinsa, ko kuma tabbatarwarsa, wato Imam Zainul Abdin (AS) ya gan su a wannan shiga ta bakaken kaya baki dayansu, wato abin da ake so a fitar a nan shi ne; wannan Sunnah ta shiga babin tabbatarwa. Haka nan baya ga wannan daga cikin gudummuwar da suka bayar shi ne Tablig din ita wannan waki’a wato isar da ita ga wadanda ba su kasance a wajen ba. Domin baki daya duk bayanan da ake yi da rubuce-rubucen da ake yi dangane da wannan waki’ar ta Karbala, wato abubuwan da suka auku a ranar Ashura da kuma abubuwan da suka biyo baya, duk daga wajen su aka ji.
Wannan yana daya daga cikin asrar da kuma hikima Ilahiyya da ya sa Imam Husain (AS) ya tafi da mata da kuma yara cikin wannan waki’ar kamar yadda wasu Malamai suka tafi a kai, wato saboda su isar da wannan waki’ar ga mutanen zamaninsu, da ma wadanda za su zo daga baya na abubuwan da idonsu ya gani, kunnuwansu suka ji da kuma abubuwan da suka fuskanta a Karbala da Kufa da kuma Sham. Kuma a kan wannan asasi na tablig din wannan waki’ar ta Karbala wanda Sayyidah Zainab (AS) ta dinga yi bayan komawarta Madina, ya sa Gwamnan Madina na lokacin ya aika wa Yazid cewa, in yana da bukatar Madina, to ya kori Zainab (AS) daga cikinta, wato saboda bayanan da take yi na waki’ar yadda yake tasiri a zukatan mutane, wanda wannan tasirin ya kai ga hatta magoya bayan Banu Umayya, suka canza tunani, suka yi masu tawaye. A takaice dai Yazidu ya aika da umurnin a kore ta daga Madina, shi ya sa in muka duba za mu ga kabarinta ba a Madina yake ba.
Daga cikin gudummuwar da mata suka bayar a wannan waki’ar ta Karbala. Akwai kula da kuma ba da magani ga wadanda suka samu raunuka, wanda Zainab (AS) ta ba da gudummuwa babba a wannan fage. A kan asasin haka ne ma a Jamhuriyar Musulunci ta Iran aka bai wa ranar da aka haifi Zainab (AS) sunan “Ranar masu kula da majinyata”, don tunawa da girmama irin gudummuwar da ta bayar wajen jinyar wadanda suka samu raunuka a Karbala.
Daga cikin gudummuwar da mata suka bayar a cikin wannan waki’ar ta Karbala ita ce karfafa mazajensu da kuma ’ya’yansu, wajen taimaka wa Imam Husain (AS).
Ga misali matar Zuhair kamar yadda ya zo a tarihi Zuhair a farkon al’amarin ya so ya kasance ba su hadu da Imam Husain (AS) ba, sai Imam Husain ya aika yana kiran sa.
Lokacin da wannan sako ya zo ga Zuhair sai ya yi dan nauyin jiki ga amsa wannan kiran, sai matarsa ta karfafa shi a kan ya tafi ya amsa kiran Imam Husain (AS) ya ji menene, bayan ya tafi ya dawo, ikon Allah sai ya dawo da canjin tunani da kuma yankewa cewa zai shiga cikin rundunar Imam Husain (AS). Shi ne matarsa ta ce masa; “Allah (T) ya yi maka zabi. Ina rokon ka, ka tuna da ni wajen Kakan Husain (AS) ranar kiyama”.
Haka nan Zainab ta ba da gudummuwa mai yawa wajen karfafa zukatan wadanda suka yi musharaka a cikin wannan waki’ar ta Karbala, musamman ma mataye da yara a bayan shahadar su Imam Husain (AS). Daga cikin gudummuwar da mata suka bayar a wannan waki’ar ta Karbala akwai niyya da kuma azama wajen sadaukar da kai domin taimaka wa Imam Husain (AS). Idan mutum ya bibiyi tarihin wannan waki’ar, zai ga akwai matayen da suka yi yunkurin fafatawa da makiya, Imam Husain (AS) ya ce su koma.
Misali wata mata mai suna Ummi Wahab, lokacin da mijinta ya fito yana fafatawa da makiya ita ma ta yunkuro domin ta shiga fagen faman a fafata da ita, sai Imam Husain (AS) ya ce, ta koma hema. Ya ce mata Allah ya saka da alheri. Bayan shahadan mijin nata ta shigo filin daga tana share masa jini, tana ce masa; “Albishirinka da Aljanna, ina rokon Allah da ya azurta ka da Aljanna ya sa ni danshinka mu tafi tare”.
Tana cikin fadin haka sai Shimr ya ba da umurnin a rotsa mata kai, aka ko aiwatar da umurninsa na rotsa mata kan. Nan take Allah ya yi mata rasuwa. Saboda haka ita ce farkon matar da aka kashe a cikin wannan waki’ar ta Karbala.
Shi ne bayan da Mahaifiyar wannan Shahidi ta ga danta an kashe, ga matarsa an kashe, ta dauki makami ta yunkuro domin ta shiga fagen fama ta fafata da makiya. Imam Husain (AS) ya ce ta koma. Shi ne ta koma tana cewa ya Allah kada ka yanke fatana, wato na samun shahada. Sai Imam Husain (AS) ya ce; “Allah ba zai yanke maki fata ba”. Da dai misalan irin wannan da yawa, wanda ba za a kawo ba saboda gudun tsawaitawa, wato irin wannan gudummuwar da mata suka bayar wadanda aka ambata da ma wadanda ba a ambata ba.
Akwai kuma dauriya da dakewa da suka yi na fuskantar wahalhalu daban-daban ta kuma fuskoki da daban-daban tun daga ranar Ashura har bayan shahadar su Imam Husain (AS) har ya zuwa dawowar su Madina. Ga kulasar matsalolin da suka fuskanta tun daga ranar Ashura har zuwa dawowar su Madina. Sai dai abubuwan suna da sosa rai da kuma ta da hankali. Bayan da aka kashe dukkan Sahabban Imam Husain (AS) da kuma Bani Hashim, ya zama yanzu babu wani namiji babba da ya rage face Imam Zainul Abidin (AS), shi kuma bai da lafiya, da kuma mata da yara, sai Imam Husain (AS) ya tafi domin ya yi bankwana da su. Abu na karshe da ya fada wa Imam Zainul Abidin (AS) da ya yi bankwana da shi, shi ne ya ce masa; “Ya kai dana! Ka isar da sallamata ga Shi’ata (wato mabiyana) ka ce masu, babana an kashe shi yana bako. Saboda haka ku yi juyayi, ku yi kuka”. Bayan nan ya tafi hema wato tanti na su Zainab (AS) domin ya yi bankwana da su. Ya kira sunansu daya bayan daya; “Ya Sukaina! Ya Fadima! Ya Zainab! Ya Ummul Kulsum!” Haka ya kira su dukkan su ya ce masu; “Amincin Allah ya tabbata a gare ku, wannan ita ce karshen haduwa ta da ku”. Wato a wannan gida na duniya). Jin haka nan take dukkan su suka fashe da kuka. Ya ce masu; “Ku yi shirin fuskantar jarabawowi.
Amma ku sani Allah (T) zai kiyaye ku, zai kuma kiyaye mutuncinku, kuma zai tseratar da ku daga sharrori na makiyanku”.
Kuma in muka duba mutum zai ga cewa wannan abin ya tabbata, wato duk da yadda suka kasance a hannun makiya masu busassun zukata da kuma yunkurin da Ibn Ziyad ya yi na ya kashe Zainab (AS), da kuma wanda Yazid ya yi na ya kashe Imam Sajjad, duk Allah ya kiyaye su da ma yunkurin da wani mutumin Sham ya yi a fadar Yazid na cewa a ba shi Fatima ’yar Husain (AS), shi ma Allah ya kiyaye. Wahalhalu kam sun sha na yunwa da kishin ruwa da duka na tafiyarsu daga Karbala zuwa Sham. Amma kisa da taba mutunci, Allah (T) ya tsare kamar yadda Imam Husain (AS) ya shaida masu.
Karshen abin da Imam Husain (AS) ya ce wa Zainab (AS) a wannan bankwana shi ne ya ce mata; “Ya ’yar uwata kada ki manta ni a Sallar dare (wato sashe cikin addu’a) domin ya zo a tarihi cewa Zainab (AS) hatta ranar Ashura da daddare ba ta bar Sallar tahajjud dinta ba, duk da ko ga shi a daren Ashura sun kwana suna ibada, a ranar Ashura kuma ga abubuwan da suka faru, amma duk da haka, haka ta yi Sallar dare amma a zaune saboda gajiya da yunwa da kishi. Shi ne har Imam Zainul Abidin yake tambayar ta dalilin Sallar a zaune ta ce masa; “Wallahi kafafuwana ba su iya dauka ta”. Bayan haka Imam Husain (AS) ya fito zai wuce ya duba dama ya duba hagu ba kowa ya ce; “Wa zai kawo min doki?” Da Zainab da ta ji haka, ta fito ta je ta zo masa da dokinsa (AS), ya hau ya tafi fagen fama.
Abubuwan da suka faru suka faru marasa dadin ji da karantawa da kuma rubutawa, wato na abubuwan da Shimril (LA) ya yi masa. Can bayan wani lokaci sai ga doki ya dawo zuwa tantin su Zainab (AS) ba Imam Husain (AS), wanda abin da yake alamta an kashe Imam Husain (AS).
Wannan doki ainihinsa dokin Manzon Allah(S) ne, amma ikon Allah ya yi masa tsawon rai har zuwa lokacin wato bayan shekara 50 da rasuwar Manzon Allah (S) yana raye. Bayan wadannan la’annanun sun kashe wadannan bayin Allah, sai suka bi su suna daddebe masu tufafin jikinsu suna rabawa tsakaninsu. Haka suka bar su babu tufafi a jikinsu. Ya ma zo a kan cewa kasantuwar Imam Husain (AS) ya san haka za ta auku, da zai fita bayan ya yi bankwana da su Zainab (AS ya samu tsofaffin tufafi wanda mutum ma ba zai yi sha’awarsu ba ya sa. Saboda wannan mummunan aiki da za su yi. Haka bai ishe su ba, sai suka bi su suka sasssare kawukansu daga jikunansu, shi ma suka raba kawukan tsakaninsu. Daga karshe wanda ya jagoranci yakin baki daya ya ba su umurnin da su hau dawakansu su yi sukuwa a kan jikkunan wadannan bayin Allah!! Haka ko suka aikata wannan mummunan aikin.
Bayan haka sai suka tafi hemomi na mata da yara da suka rage suka kwashe masu kayyakinsu!! Kai hatta dan kunne na mata da ababen hannu irin su warwaro ba su bari ba. Wani ma da ya je hemar da Imam Sajjad (AS) yake ciki yana jinya, shimfidar da Imam Sajjad yake kai, ya fisge ya jefar da Imam Sajjad (AS) a kasa. Ana cikin haka sai ga Shimr ya zare takobi zai sara wa Imam Sajjad (AS), sai Zainab (AS) ta fada kan Imam Sajjad (AS) ta ce sai dai a kashe ta kafin a kashe shi. Nan dai wasu suka ba da baki cewa a kyale shi, shi ne Shimr (LA) ya ce masu ai kun san abin da Ibn Ziyad ya ba da umurni a kan cewa a kashe duk ’ya’yan Husain (AS). Allah(T) bisa ikonsa ya tsare.
Bayan sun gama wannan aika-aika na kwashe kayayyakin wadannan matan da kuma yara, sai suka cinna wa tantunan wuta. Shi ne Zainab (AS) ta samu Imam Sajjad ta shaida masa ga abin da mutanen nan suka yi na sa wa hemomi wuta.
Meye abin yi? Imam Sajjad (AS) ya ce su fita daga cikin hemomin su gudu. Bayan da suka gama wannan aika-aikan na kona tantuna, Zainab (AS) ta sake tattara wadannan bayin Allah (T) da yara a waje daya. A cikin wannan yanayin ne aka samu yara biyu suka rasu ’ya’yan Khadija ’yar Imam Ali (AS), sakamakon yunwa da kishi da kuma firgitar da yara da suka yi. Haka wadannan bayin Allah suka kasance a filin Allah (T) har wayewar gari. Haka Zainab (AS) ta kasance lokaci bayan lokaci tana bi tana dudduba su. Saboda a wannan rana ta Ashura bayan shahadar su Imam Husain (AS) mafi yawan wahalhalun da wadannan bayin Allah suka fuskanta Zainab ce ta fi kowa shan wahala a cikinsu, saboda ya zo a kan cewa sun dake ta ba kadan ba, don ko duka za a kai wa wani cikin mata da yara ita ta karewa da jikinta. Haka suka kwana a daren 11 ba abinci, ba ruwa, ba kayansu da suke amfani da shi yau da kullum, duk an kwace.
Kaduna Press
2022/1444H
0 Comments