A ranar Asabar 15/1/2022 da ta gabata Sister forum Almajiran Sayyid Zakzaky (H), Na Halkar Rasulul-Akram Kaduna sun Gudanar da Mauludin Sayyida Zahara (SA), Unguwar Mu'azu, An fara taron ne da Addu'ah Sai karatun Alqu'rani mai girma tare da ziyaran Sayyida Zahara (SA),
Sannan a ka Gudanar da wakokin yabo ga Sayyida, Sai a ka gabatar da mai jawabi.
Malama Fatima Muhammad (Mujahida)
Tagabatar da jawabi mai taken rayuwan Sayyida Zahara a gidan Mijinta, Malamar ta tabo wasu janibobi da dama, inda take cewa: duk wani abun da a ke nima na tarbiya to za a same shi ne acikin rayuwan sayyidah Zahara.
Sanan tace: sayyida mace ce mai hidimtama mijida, bawai sai tajira daga mijinta ba, haka nan ta fuskacin hakuri nan ma sayyida ta daban ce, ta dace da dukkanin sunayen da a ka kirata da su.
Sannan a ka mika abin magana ga wakilin Almajiran Sayyid Zakzaky na garin Kaduna, Sheikh Aliyu Umar (Tirmizi) in da ya yi ta'aliki, inda ya ke cewa: inda duk zamuyi koyo da rayuwar Ahlul-bayt (As) to da mun zama waliyan wannan zamanin.
Daga karshe an yanka alkaki, a ka raba walima , a kayi Addu'ah a ka sallami kowa.
Ga Wasu Daga Cikin Hotunan Da Muka Dauko Muku A Wajan.
-Kaduna press
©15/1/2022
0 Comments