- Kaduna Press
©18/1/2022
15/6/1443H
Kamar yadda a ka saba yau Talata 18/1/2022 da misalin karfe biyu (2:00pm) na rana Sisters forum Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H), Halkar Imam Hassan kaduna sun gudanar maulidin yar Manzon Allah (S) wato Sayyid Fatima Az-Zahra (S.A) a ungwar Nasarawa Kaduna.
Bayan bude taro da Addu'ah da karatun Alqur'ni, wakokin yabo da ga sha'irai, sai ka karanta Ziyarar ga Sayyid (S.A).
Sai kuma a ka gabar da mai jawabi Sidi Fasihul Nisan in da ya gabatar da jawabi mai taken matsayin Sayyida Zahra (S.A) a wajen Allah, Mallam ya tabo wasu rayuwa da ga ayoyin Qur'ani in da Allah ya ke cewa: Girman matsayinta gun Allah zaka duba.
Sabo da ita Sayyida Zahra garanto ce ga duk wanda zai shi ga aljanna.
Bari kaji watarana Annabi yazo gidan Fatima sai ya tambaya ko kina da abinci?
sai Sayyida tace: Babu komai ya Abbana a gidanan sai ya tashi domin ya karasa gida
sai a ka ga Sayyida Zahra ta shiga daki tana rokon Allah tace: ya Rabbi Kaine kaciyar da bayi da abinci daga sama nima Allah kaciyar Dani, Kafin wani lokaci kadan sai ga abinci kala kala daga sama, sai ta tura a ka kira Annabi Muhammad (s. w . a) Sai tabashi Sai yace: Ina Ki ka samo wanan abinci haka cikin karamin lokaci kafin na i sa gida? gashi kala kala, Sai tace: yanzu Mala'ika ya kawo min daga sama.
Wanan kenan ya kamata mutane mu gane wacece Yar Annabi, sanan muyi hidima sosai a gareta.
Duk da wanan da mukeyi ga kujeru ga abun kwalliya ga kuma abinci duk albarkacinta, to muyi dan Allah.
A ka mika a bun magana ka wakilin Almajiran Sayyid Zakzaki na garin Kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi) in da ya gabatar da Ta'alik.
Daga nan sai a ka gabatar da walima, a ka raba kyaututtuka a ka yi addu'ah, ka sallami kowa.
- Kaduna Press
©18/1/2022
15/6/1443H
0 Comments