- Kaduna Press
©20/1/2022
17/6/1443H
Bayan bude taro da Addu'ah da karatun Alqur'ni, sai ka shiga filin mawaka, sannan a ka karanta Ziyarar ga Sayyid (S.A), Faretin girmamawa gareta.
Sai kuma a ka gabar da mai jawabi na farko Sidi Fasihul-Nisan a cikin jawabin sa Malam ya kawo falala da darajojin Sayyida Fatima (S.A), sannan ya kawo wani kissa na wani Dattijo ya zo wajen Manzon Allah (Saww) tare da yi masa bayanin halin da yake ciki na kuncin rayuwa na rashin abinci da tufafi da kuma kudi.
Sai Manzon Allah (saww) ya ce: ya . gidan Fatima”.
Wannan Dattijo sai ya kama hanya zuwa gidan Sayyida Fatima (S.A) da ya je gidan ya yi sallama.
Ya shida wa Sayyida Fatima (S.A) ga halin da yake ciki na rashin abinci da tufafi da kuma kuddi, Sayyida Fatima ta shiga gida ta debe abin wuyanta, wato sarka da ta gada wajen mahifiyarta, ta kawo masa.
Sai ya amsa, bai tsaya ko’ina ba sai wajen Manzon Allah (Saww), ya same shi yana zaune tare da Sahabbai, ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) Fatima ta ba ni
wannan sarkar a kan in sayar domin in biya bukatuna”.
Sai Ammar ya tambayi wannan Dattijon a kan nawa zai sayar masa da sakar? Sai ya ce masa; “Ni dai abin da nake bukata kayan abinci da tufa ko da kuwa daya ne, da kuma Dinare, shi ma ko da daya ne da zai kai ni garinmu”.
Sai Ammar ya hada masa kayayyakin abinci da kuma tufafi da kuma dabbar da zai hau zuwa garinsu, ya kuma ba shi kudi Dinare 20.
Ammar bin Yasir daya sayi wannan sarka, ya sa mata turare na Almiski ya nade ta a wani kyalle mai kyau ya ba Bawansa ya kai wa Manzon Allah (Saww). sarkar da Bawan, duk ya ba shi.
Da ya i sa wajen Manzon Allah (Saww) ya fada masa sakon. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce je ka kai wa Fatima sarkar da wannan Bawa. Ya je wajen nana Fatima ta amshi sarkar, shi kuma Bawan, ta ’yanta shi.
Lokacin da Manzon Allah (Saww) ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce; “Wannan sarka mai albarka ta biya bukatar mabukaci (wato Dattijo) ta kuma ‘yanta bawa, ta kuma koma hannun mai ita.
Malam Ahmad Rufa'i inda ya gabatar da jawabi a kan Rayuwar Sayyida Zahra (S.A) bayan wafatin Manzon Allah (S), Mallam ya karanto hadisai in da Manzon Allah ya ke cewa: Fadimatu bid'atunminni, ya kuma ce malam hadisi duk sun kawo, irin su Nisa'i, Suyudi, Ibn kutaiba, Baihaki, da sauran su.
Sannan ya kawo mazalumiyar ta, game da dukan ta da kuma kona gidanta kwace gonar ta (Fadak) Ibn hajar yakawo a cikin hadisin sa.
Sayyida zahra tayi kuka saboda cutar da ita da a kayi da kuma banzatar da wasiyar Manzon Allah hakan yasa a ka rasa mai lallashinta sai dai Imam Ali (As)
A lokacin da yaje lallashinta yayi dai-dai da lokacin kiran Sallah shi ne yaji ance Ashadu Anna Muhammadarrasulullah sai yake cema Sayyida har yanzun baza a goge ambaton Mahaifinki ba a doron kasa kuma har abada.
A ka mika a bun magana ka wakilin Almajiran Sayyid Zakzaki na garin Kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi) in da ya gabatar da Ta'alik. Malam ya fara ne da mika godiya ga Allah, da taya malarta taron murnar wannan rana, sannan ya baiwa jama'a hakuri dangane da abun da sukaji, ka kara da cewa: wannan waje ya tara jama'a masu banbancin fahimta, wani zai ji abin da nauyi, amma ya kamata jama'a in sunji ance kaza! A wajen maulidi to suyi bincike.
Sannan ya yayi karin haske game da gwagwar-mayar Sayyida Fatima na tinkara azzalumi, ta hanyar bijera masa (Bara'a) ko da bazai dawo maka da hakkin ka ba, ka nunawa duniya shi azzakumi ne.
Daga karshe an gabatar da walima, a ka raba kyaututtuka a ka yi addu'ah, ka sallami kowa.
- Kaduna Press
©20/1/2022
17/6/1443H
0 Comments